Wata Mata Ta Siyar da Jikanta Kan Kudi N50,000 a Anambra
- Wata mata mai suna Oluchukwu Nwosu ta siyar da jaririn jikanta ɗan watanni uku a duniya kan kuɗi N50,000
- Matar wacce ta ce jaririn an haife shi ba ta hanyar aure ba, ta siyar da siyar da shi ne saboda talaucin da ya yi mata katutu
- Hadimar kwamishiniyar mata da walwalar jama'a a jihar ta tabbatar da cew an ceto jaririn tare da cafke masu hannu a siyar da shi
Jihar Anambra - Wata mata ta siyar da jikanta mai watanni uku a duniya a kan kuɗi N50,000 a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Wacce ake zargin Oluchukwu Nwosu ta siyar da jaririn ne ba tare da sanar da ɗiyarta Ijeoma ba, wacce ta haifi yaron ba tare da aure ba, cewar rahoton Premium Times.
Chidinma Ikeanyionwu, hadimar kwamishiniyar mata da walwalar jama'a a jihar, Ify Obinabo, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba.
Ikeanyionwu ta ce a yanzu kwamishinan ta ceto yaron, sannan ta kuma taimaka wajen sanya ƴan sanda cafke wacce ake zargin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ta siyar da jaririn?
Wacce ake zargin, Mrs Nwosu, da take magana bayan ta shiga hannu, ta yi iƙirarin cewa halin talauci da kasa kula da jaririn ne ya tilasta mata siyar da shi.
Matar ta ce wannan shi ne karo na uku da diyarta ta haihu ba tare da aure ba, inda ta yi nuni da cewa akwai wasu yara biyu dukkaninsu maza, ana kula da su a wani gidan marayu da ke birnin Awka.
Ta ce tun daga lokacin da diyarta ta haifi yaron da ƙyar suke samun abin da za su ci, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya
An sake siyar da jaririn a kasuwa
Ta yi iƙirarin cewa wani mutum mai suna Tochukwu Asiegbu ya tuntuɓe ta inda ya amince ya sayi yaron a kan farashin N50,000.
A nasa ɓangaren, Mista Asiegbu, wanda aka ruwaito ya sake sayar da yaron, ya ce ya samu ribar Naira 30,000 ne kawai daga siyan jaririn.
Sai dai Evelyn Egwuatu, wacce aka ɗauko jaririn daga hannunta, ta ce ta biya wata mata Ebelechukwu Uba kudi N200,000 domin ta siyo yaron.
An Tsinci Jariri Cikin Tsumma
A wani labarin kuma, mutane da dama sun ɗimauta bayan an tsinci wani jariri kwance a cikin tsumma a Kaduna.
Jaririn an tsincesa ne babu komai a jikinsa face ƙunzugu inda yake cikin wani mawuyacin hali.
Asali: Legit.ng