Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 9 a Wani Sabon Hari a Jihar Katsina
- Ƴan bindiga sun kai wani ƙazamin hari a garin Danmusa, hedikwatar ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina
- Miyagun ƴan bindigan dai sun kai farmakin ne a daren ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba inda suka halaka mutum tara
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa bayan ƴan bindigan sun kwashe sa'o'i suna cin karensu babu babbaka, sun yi awon gaba da mutane masu yawa
Jihar Katsina - Wasu ƴan bindiga masu yawa sun kai farmaki garin Danmusa hedikwatar ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina, inda suka kashe mutum tara.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Daily Trust cewa ƴan bindigan sun kai hari garin ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba.
Yadda harin ya auku
Da Dumi-Dumi: Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Mummunan Hari Kan Jami'an Tsaro, Sun Salwantar da Rayuka
A cewarsa sun kwashe tsawon sa'o'i suna cin karensu babu babbaka inda suka kashe mutum tara ciki har da ɗan sanda guda ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ƴan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutane da dama waɗanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba, tare da jikkata wasu masu yawa.
Ya ƙara da cewa maharan sun kai farmakin ne gida-gida, inda suka yi awon gaba da wasu kayayyaki masu daraja.
Wani majiya a garin ya ce biyu daga cikin wadanda aka kashen makwabtansa ne, inda ya ƙara da cewa an kashe ɗan sandan ne bayan sun ga kakinsa a cikin gidansa.
"A halin yanzu mua shirya gawarwakinsu domin yi musu jana'iza." A cewarsa
Ya kuma ƙara da cewa kimanin mutum bakwai ne aka yi garkuwa da su.
Ƴan bindigan sun zo ɗaukar fansa
Wasu majiyoyi da ba a tabbatar da su ba a cikin al’ummar yankin sun ce mai yiwuwa ƴan bindigan sun zo ɗaukar fansa ne domin sabbin jami'an tsaron da gwamnatin jihar ta ƙaddamar sun kama tare da kashe wani shugaban ƴan bindiga.
A cewar majiyar:
"Akwai wani shugaban ƴan bindiga da ke kusa da ƙauyen Katsira wanda ya yi alfaharin zai kawar da sabbin jami'an tsaron. Nan da nan suka haɗa kai suka kashe shi."
"Lamarin ya auku ƴan kwanaki kaɗan da suka wuce, shi ya sa muka yi amanna cewa cewa yaransa ne suka kawo harin."
Menene abin da jami'an tsaro suka ce?
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, wanda ya tabbatar da aukuwar harin na daren jiya, ya ce mutum biyar ne aka halaka a harin.
Sai dai, lokacin da Legit Hausa ta kira shi domin samun ƙarin bayani dangane da harin, ya bayyana cewa jami'an rundunar sun bazama ceto mutanen da aka sace tare da cafko miyagun da suka kawo harin.
Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Uku a Kebbi
A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Kanzanna na ƙaramar hukumar Bunza ta jihar Kebbi, inda suka halaka mutum uku.
Gwamna Nasiru Idris na jihar ya ziyarci ƙauyen da lamarin ya auku inda ya bayar da kyautar N7m ga waɗanda harin ya ritsa da su.
Asali: Legit.ng