Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 3 a Wnai Sabon Hari a Jihar Kebbi

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 3 a Wnai Sabon Hari a Jihar Kebbi

  • Miyagun ƴan bindiga sun kai sabon farmaki a ƙauyen Kanzanna cikin ƙaramar hukumar Bunza ta jihar Kebbi inda suka halaka mutum uku
  • Jama'ar yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta tura ƙarin jami'an tsaro zuwa yankin domin kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga
  • Gwamna Nasir Idris na jihar ya ziyarci ƙauyen inda ya rabawa iyalan waɗanda aka kashe N3m, ya ba al'ummar ƙauyen N3m da wasu hakimai biyu N1m

Jihar Kebbi - Wasu ƴan bindiga sun kashe mutum uku a ƙauyen Kanzanna da ke gundumar Tilli a ƙaramar hukumar Bunza ta jihar Kebbi a ƙarshen mako.

Shugaban ƙaramar hukumar Bunza, Alhaji Umar Mohammed Gwade, shi ne ya shaida wa gwamna Nasiru Idris a ziyarar da ya kai ƙauyen da lamarin ya shafa, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Omokri Ya Fallasa Katobar Buhari, Ya Fadi Abin da Yan Najeriya Za Su Yi Masa da Sun San Yadda Ya Lalata Kasa

Yan bindiga sun halaka mutum uku jihar Kebbi
Yan bindiga sun halaka mutum uku a wani hari a jihar Kebbi Hoto: theguardian.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ƙauyukan ƙaramar hukumar sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga kafin na baya-bayan nan.

Wacce buƙata jama'ar yankin ke da ita?

Ya buƙaci gwamnati da ta tura jami'an tsaro a yankin domin kawo ƙarshen hare-haren da ake yawan samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya buƙaci jami'an tsaro da su kara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro a jihar.

Ya kuma yi kira ga jama'a da su tallafa wa jami'an tsaro da sahihan bayanan sirri domin murƙushe ƴan bindigan.

Hakimin Tilli, Alhaji Mohammed Jabbo, ya shaida wa gwamna Idris cewa harin ya yiwu ne saboda ƙaramar hukumar Bunza ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin.

Gwamna Idris ya bayar da tallafi

Gwamna Idris a ziyarar da ya kai ƙauyen da lamarin ya shafa ya bayar da tallafin N3m ga iyalan mutum ukun da suka rasa rayukansu, N3m ga al’ummar yankin, da kuma N1m ga hakimai biyu, rahoton TheCable ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Tinubu vs Atiku: Tsohon Jigon Jam'iyyar APC Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga Alkalan Kotun Koli

Jihar Kebbi na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro.

Shugaban Hukumar Tsaro Ya Ajiye Aiki

A wani labarin kuma, shugaban kwamitin kafa jami'an sa kai domin samar da tsaro a jihar Sokoto, Kanal Garba Moyi, ya yi murabus daga muƙaminsa jim kaɗan bayan an rantsar da shi.

Kanal Garba wanda bai bayyana dalilin yin murabus ɗin nasa ba dai, ya ajiye muƙaminsa ne ƴan sa'o'i bayan an rantsar da kwamitinsa mai mambobi mutum 25.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng