'Yan Sanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi da Yiwa Dattijuwa Kisan Gilla a Jihar Gombe
- 'Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da kashe wata maia mai shekaru 58 a unguwar Jeka da Fari da ke birnin Gombe
- A watan Agusta wasu 'yan ta'adda suka shiga har gida suka kashe malamin addini a unguwar Tabra
- Jihohin Arewa na yawan fama da barnar 'yan ta'adda da matasa masu kwacen waya da sace-sace
Jihar Gombe - Rahoton da muke samu daga jihar Gombe ya bayyana cewa, an kama wasu tsagerun da ake zargi da kashe wata mata mai shekaru 58 a jihar.
A baya Legit Hausa ta kawo maku cewa, an yiwa wata mata mai suna Aishatu Abdullahi kisan gilla a unguwar Jeka da Fari da ke tsakiyar jihar.
Tun bayan alanta mutuwar matar, 'yan sanda suka fara bincike don kamo wadanda ake zargi da wannan bakin aiki.
An ga nasarar kame 'yan ta'addan
A wata sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Gombe, ASP Mahid Muazu Abubakar, Anipr ya fitar, ya ce jami'ai sun kai ga nasara a binciken da suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
"'Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da kashe dattijuwa mai shekaru 58, Aishatu Abdullahi (Adda Damori), sa'o'i 48 bayan aukuwar lamarin."
Sai dai, ya zuwa yanzu bai bayyana sunayen wadanda ake zargin ba, kana bai yi karin haske kan yadda bincike ya kai kama su ba.
Legit Hausa na ci gaba da dakon abin da ka iya biyo baya na bayanan wadanda ake zargi da wannan danyen aikin.
Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fama da barnar 'yan ta'addan da ke shiga gidaje tare da kashe mutane babu gaira babu dalili.
An yi ajalin malamin addini a Gombe
Dattijuwa Ta Rasa Ranta Bayan 'Yan Ta'adda Sun Yi Mata Yankan Rago a Jihar Arewa, 'Yan Sanda Sun Yi Martani
A wani labarin na daban, mun kawo maku labarin yadda wasu da ake zargin barayi ne suka yi ajalin malamin addini a Gombe, Sheikh Ibrahim Musa (Albanin Kuri) a gidansa da ke Tabra bayan garin Gombe.
Barayin sun yi ajalin malamin ne a daren Talata 8 ga watan Agusta yayin da suka shiga sata a gidan marigayin.
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka aikata laifin da kuma daukar matakin kare aukuwar irin hakan a gaba.
Asali: Legit.ng