Wike: Tsohon Kakakin APC Ya Nemi a Kama Sheikh Gumi
- Tsohon mataimakin sakataren labaran jam'iyyar APC na kasa, Yekini Nabena, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya kama shahararren malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi
- A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Nabena ya yi kira ga kama Gumi kan furucin da ya yi game da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike
- Sheikh Gumi dai ya kira Wike da shaidani saboda ya tarbi ambasadan Isra'ila a Najeriya sannan ya yi taron manema labarai a ofishinsa
FCT, Abuja - Yekini Nabena, tsohon mataimakin sakataren labaran jam'iyyar APC na kasa, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya kama Sheikh Ahmad Gumi, shahararren malamin Musulunci mazaunin Kaduna.
Jigon na APC ya yi kira ga shugaban kasar da hukumomin tsaro a kasar da su kama malamin musuluncin kan furucin da ya yi kwanan nan a kan Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya.
A cikin wata sanarwa da aka aikewa Legit Hausa a ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba, Nabena ya yi Allah wadai da furucin malamin musuluncin, cewa shi da wasu masu nuna kabilanci da wasu masu ra'ayin rikau na addini a arewacin Najeriya suna da nuna isa.
Shugabannin Niger Delta sun aika sakon gargadi ga Gumi kan furucinsa game da Wike
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma yi gargadin cewa idan wani abu ya faru da Wike a iya lokacin da zai yi kan kujerar ministan Abuja, toh Sheikh Gumi da irinsa mutanen Niger Delta za su rike.
A ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba ne Sheikh Gumi ya kira ministan da "shaidanin mutum" kan tarban ambasadan Isra'ila a Najeriya da kuma ba shi damar yin taron manema labarai a ofishinsa.
A cikin bidiyon mai tsawon mintuna 14 da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gumi ya yi hasashen cewa shugaba Tinubu ba zai mulki kasar na tsawon shekaru takwas ba.
Jigon na APC wanda yake haifaffen jihar Bayelsa ya ce:
"Jin kai na wasu yan arewa ba wai kawai raba kasar yake ba illa yana sa su ga yan kudu a matsayin na kasa da su a kasar da ya kamata kowa ya samu yanci iri guda."
Sheikh Gumi ya bude asusun ba da gudunmawa ga 'yan Falasdinu
A wani labarin, mun ji cewa Sheikh Ahmed Gumi ya bude asusun da za a yi amfani da shi don taimakawa Falasdinawa yayin da ake ci gaba gwabza yaki.
Gumi ya bayyana cewa za su yi wannan aiki ne don taimakawa mutanen Falasdinu yayin su ke cikin wani yanayi na zalunci daga Isra’ila.
Asali: Legit.ng