Kwankwaso Zai Taimaki Almajirai Masu Karatun Allo a Kano
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana wani sabon shirin ba almajiran da suka yi karatun allo, tallafi a jihar Kano
- Kwankwaso ya yi nuni da cewa za a samo aƙalla almajirai 100 da suka sauke Al-Qur'ani mai girma a sanya su a makaranta su samu ilmin boko
- Da sun kammala karatu a matakin firamare da sakandare, Kwankwaso ya ce za a tura su jami'o'i na cikin gida da ƙasashen waje domin faɗaɗa karatunsu
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana shirinsa na taimakawa almajirai masu karatun allo, su yi karatun Boko a jihar Kano.
Ɗan takarar na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya yi nuni da cewa za su fara wannan shirin ne da almajirai guda 100 waɗanda suka sauke Al-Qur'ani mai girma a karon farko.
Yadda shirin zai kasance
Kwankwaso wanda ya bayyana hakan a cikin wata hira da aka yi, ya bayyana cewa idan aka zaɓo waɗanda suka cancantan, za a ware iya lokacin da za su yi karatu a makarantun firamare sakandire.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa waɗanda za a zaɓo din, za su yi shekara ɗaya suna karatu a matakin firamare, sannan su ƙara yin wata shekara ɗaya a matakin sakandare. Ya ce za ayi musu hakan ne domin dama kwakwalwarsu a buɗe take da ilmi.
Shirye-shirye sun yi nisa domin aiwatar da wannan aikin inda nan ba da daɗewa ba za a fara ɗibar sahun farko na aƙalla mutum 100, waɗanda za a fara shirin da su.
A yayin gudanar da shirin, Kwankwaso ya yi nuni da cewa za su riƙa ba ɗaliban tallafin abinci, sannan bayan sun kammala shekara biyun, za a tura su zuwa jami'o'in ƙasar nan da wasu a ƙasashen waje domin su yi karatun digiri.
Legit Hausa ta nemi jin ta bakin Ibrahim Ado, hadimin tsohon gwamnan na jihar Kano domin samun ƙarin bayani kan yadda tsarin shirin zai kasance.
Sai dai, bai ɗauki kiran da aka yi masa a waya ba, sannan bai dawo da saƙon da aka tura masa ta waya ba.
Kwankwaso Ya Shawarci Wadanda Aka Yi Wa Auren Gata
A wani labarin kuma, Rabiu Musa Kwankwaso ya aike da shawara ga mai muhimmanci ga ma'aurata kan yadda za su zauna lafiya a gidajen aurensu.
Kwankwaso ya shawarci ma'auratan da su guji duba wayoyin abokan zamansu idan suna son aurensu ya yi ƙarko, domin duba waya na kashe aure sosai a wannan zamanin.
Asali: Legit.ng