Abin da Cire Takunkumin CBN Yake Nufi a Kan Tattalin Arziki da Farashin Kaya, Masani

Abin da Cire Takunkumin CBN Yake Nufi a Kan Tattalin Arziki da Farashin Kaya, Masani

  • Bankin CBN ya soke tsohon tsarin da ya kawo a baya, yanzu babu takunkumi wajen shigo da kaya daga kasashen ketare
  • A ra’ayin CBN, wannan mataki zai farfado da tattalin arziki tare da samar da aikin yi da gyara kasuwar canjin kudin waje
  • Mun yi hira da Dr. Usman Bello daga jami’ar ABU Zariya, ya nuna mana ba dole ba ne abinci ya yi sauki ko Dala ta yi araha

Abuja - babban Bankin Najeriya, CBN ya sanar da cire takunkumi wajen bada dala domin shigo da wasu kayayyaki 43 wanda a baya bankin ya cire hannu a kan su.

Punch ta ce kungiyar OPS ta ‘yan kasuwa ta yabawa wannan mataki, ta na mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi a Najeriya.

A wata sanarwa da bankin na CBN ya fitar a makon jiya, ya ce janye takunkumin zai rage adadin masu neman kudin kasar waje a kasuwar canji.

Kara karanta wannan

Babban Kuskuren Da Tinubu Ya Ke Tafkawa, Ya Haddasa Tashin Dala a Yau - Masani

Bankin CBN
Sababbin Gwamnonin CBN Hoto @Cenbank
Asali: Twitter

Tsarin zai tabbatar da ‘yan kasuwa su ke juya farashin kudin ketare, kuma ana sa ran samun sauki wajen yadda farashi ya ke canzawa bini-bini.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan zai sa abinci ya rage tsada?

A hirar da Legit Hausa ta yi da Dr. Usman Bello, ya shaida mana watakila CBN sun yi haka ne saboda ayi maganin masu yawan boye kayan abinci.

Idan babban bankin zai bada kudi domin shigo da irinsu shinkafa daga kasashen waje, masana su na tunanin yawa zai jawo farashi ya karye.

Dr. Usman Bello wanda masanin tattalin arziki ne a jami’ar ABU Zariya ya ce ba dole hakan ta faru ba, la’akari da farashin Dala-Naira a halin yanzu.

"Ba zai yi tasiri ba idan sai an saye dala da tsada, tun da babu rangwame, farashi ba zai canza ba, ‘yan kasuwa za su ji kyashin shigo da kaya."

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tsageru sun yi yunkurin kashe gwamnan APC a Arewa, bayanai sun fito

Dala za ta yi sauki ko tsada?

"Muddin babu saukin da masu kawo kaya daga kasashen waje za su samu daga CBN, Dala za ta iya kara tashi a maimakon Naira ta mike."

- Dr. Usman Bello

‘Yan kasuwan da za su amfana da damar da aka bude za su yi sanadin tashin farashi saboda rububin da za a kara yi wajen neman kudin ketaren.

Daga lokacin da aka sanar da tsarin zuwa yau, dalar Amurka ta tashi da kusan N200, Dr. Bello ya ce an saida dala a BDC kan fiye da N1175 a jiya.

Nawa Dala ta ke a kasuwa?

Duk da dabarun da CBN ke yi, Dalar Amurka na jijjiga Naira a kasuwar canji, rahoton karshe ya nuna an saida Dala a kan fiye da N1, 000 a kasuwa.

Sabon gwamnan bankin CBN ya na kokarin ganin an kara sakin daloli domin naira ta huta, sai dai har yanzu abubuwa kara cabewa su ke ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng