"Mun Rasa DPO da Wasu Jami'ai Biyu a Harin Yan Fashi a Benue" Yan Sanda
- Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa an kashe DPO da wasu yan sanda uku yayin harin yan fashi da makami a jihar Benuwai
- Mai magana da yawun rundunar reshen jihar, SP Anene, ta ce jami'an tsaro sun kashe biyu daga cikin maharan kuma sun bi sawun sauran
- A ranar Jumu'a da yamma ne wasu 'yan fashi suka shiga bankuna a garin Otukpo, inda suka shafe lokaci suna aikata ta'asa
Jihar Benue - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Benuwai ta tabbatar da cewa an kashe mata manyan jami'ai yayin harin 'yan fashi da makami a garin Otukpo.
Rundunar ta ce DPO na caji Ofis din Otukpo, CSP. John Adikwu, da wasu jami'an ƴan sanda guda uku sun rasa rayukansu yayin artabu da maharan waɗan da suka shiga Bankuna.
‘Yan fashi da makami sun tayar da hankulan mazauna Otukpo a lokacin da suka farmaki wasu bankuna da ke tsakiyar garin da yammacin ranar Juma’a.
Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Benuwai, SP. Catherine Anene, ita ce ta fitar bayanin jami'an da aka rasa a wata sanarwa ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Anene ta tabbatar da cewa yayin wannan harin, 'yan fashin sun aikata ta'adi a bankuna biyar ɗaya bayan ɗaya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
An kashe wasu daga cikin maharan
Kakakin yan sanda ta ƙara da cewa yayin bin sawun maharan, jami'an tsaro sun yi nasarar hallaka biyu daga cikin 'yan fashi da makamin.
A cewarta, har 'yanzu dakarun 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro na ci gaba da bin diddigin ragowar waɗanda suka jefar da ababen hawansu, suka fantsama cikin daji.
SP Anene ta ce:
“An tura karin tawagar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro zuwa Otukpo domin su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma hana wadannan ‘yan fashin tserewa."
Ta bayayana cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin amma duk da haka ba ta ce komai ba game da adadin fararen hula da aka kashe yayin fashin, Channels tv ta ruwaito.
Kotun Abuja Ta Raba Auren Shekara Hudu a Abuja
Kuna da labarin Wata Kotu a babban birnin tarayya Abuja ta raba auren mata da miji, ta umarci matar ta fara idda kamar yadda Musulunci ya koyar.
Kotun ta kawo karshen zaman aure tsakanin Hafsat Abdullahi da Rufai saboda matar ta ce ta daina sha'awar zama da mijin.
Asali: Legit.ng