Hotuna Sun Bayyana Yayin da Dan Yar’Adua Ya Yi Wuff Da Diyar Babandede

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Dan Yar’Adua Ya Yi Wuff Da Diyar Babandede

  • Dan tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar’Adua ya angwance da kyakkyawar amaryarsa
  • An kulla auren Ibrahim Yar’adua da amaryarsa Amira a ranar Juma’a, 20 ga watan Oktoba
  • Amaryar ta kasance diya a wajen tsohon shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Muhammad Babandede

Kyakkyawar diyar tsohon Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Muhammad Babandede, mai suna Amira ta shiga daga ciki.

Ibrahim, dan tsohon shugaban shugaban kasar Najeriya, marigayi Umaru Musa Yar'adua ne ya auri Amira, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ibrahim Yar'adua ya auri Amira Babandede
Hotuna Sun Bayyana Yayin da Dan Yar’Adua Ya Yi Wuff Da Diyar Babandede Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Dubban jama'a sun shaida daurin aure tsakanin Ibrahim da kyakkyawar amaryarsa Amira a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta rahoto, amarya Amira ce mata ta biyu a wajen Ibrahim domin dai ya auri uwargidarsa mai suna Saratu Sodangi, wadda lauya ce a shekarar 2018.

Kara karanta wannan

Ministan Abuja Ya Sake Dauko Gingimemen Aiki, Da Yiwuwar Ya Kwace Wasu Gidaje a FCT

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuni hotunan ma'auratan suka karade shafukan soshiyal midiya inda aka gano amarya da ango cikin shiga ta alfarma suna yi wa junansu kallon so da kauna.

A daya daga cikin hotunan, an gano amaryar sanye da doguwar riga irin ta amare kalar dorawa da bula kanta sauke da lullubi sannan angon ya sanya farar shadda dinkin babbar riga.

Sun kasance rike da hannayen juna suna masu kallon kwayar idanunsu wanda ke nuna shauki da kauna tsantsa.

Ga hotuna a kasa:

Sanata Barau Jibrin ya nada mai kayan mata ta zama hadimarsa

A wani labari na daban, mun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya nada Aminat Ayeni Onisiwo, mai kayan mata wacce aka fi sani da 'Aminat Secrets', a matsayin babbar mai taimaka masa a majalisa, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Bana Sha'awar Mijina" Kotu Ta Raba Auren Wata Hafsat Abdullahi da Mijinta a Abuja Kan Abu 1 Tak

Aminat, wacce ke siyar da kayan mata a dandalin Instagram, ta yada wani hoto da kannenta ke tayata murnar wannan sabon mukami da aka bata a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

Koda dai ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawan bai sanar da batun nadin nata ba, kannen Aminat sun yi mata fatan nasara a sabon aikin nata.

Aminat ta shahara sosai a sana'arta na siyar da kayan mata domin taimakawa ma'aurata yadda a su kula da zamantakewar juna ta fuskacin auratayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng