Mutum 1 Ya Rasu a Wani Hatsarin Jirgin Ruwa a Jihar Neja
- An samu aukuwar wani hatsarin jirgin ruwa mai ɗauke fasinjoji da kayayyaki a ƙaramar hukumar Katcha ta jihar Neja
- Wani ƙaramin yaro ya riga mu gidan gaskiya yayin da wasu mutum uku suka ɓace bayan kwale-kwalen ya kama da wuta
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa kwale-kwalen ya kama da wuta ne lokacin da direbansa ya tayar da injin domin fara tafiya
Jihar Neja - Wani yaro ya mutu yayin da wasu mutum uku suka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a ƙaramar hukumar Katcha ta jihar Neja.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, kwale-kwalen mai ɗauke da kaya da ƴan kasuwa ya taso ne daga garin Katcha, bayan an tashi kasuwar, inda injinsa ya kama da wuta sannan ya ƙona kwale-kwalen ƙurmus a yammacin ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.
Majiyoyi sun ce kwale-kwalen ya nufi garin Zakanti da Danbo da sauran ƙauyukan da ke bakin ruwa a jihohin Kogi da Neja tare da ƴan kasuwar da kayayyakinsu.
Yadda lamarin ya auku
Wani mazaunin garin Katcha Malam Adamu Mohammed ya bayyana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kwale-kwalen ya yi lodin fasinja da kayayyaki daga kasuwar mako-mako ta Katcha jihar Neja zuwa jihar Kogi. Direban na kunna injin domin fara tafiya, sai kawai injin ya kama da wuta wanda hakan ya sanya fasinjojin suka ruɗe."
"Sun fara tsalle cikin ruwa har da mata da yara. Har wasu mata suka riƙa jefar da jariransu. Amma an yi sa'a, tun da ba su yi nisa daga wurin tashin jirgin ba, masu iyo na cikin gida suka fara aikin ceto. Abin da ya ceci lamarin ke nan, da ba domin haka ba, da abin bai yi kyau ba."
An tabbatar da aukuwar lamarin
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban masu tuƙa kwale-kwale na Katcha, Dangana Dambo ya ce kwale-kwalen ya ƙone ƙurmus tare da wasu kayayyaki na miliyoyin Naira.
Ya ce har yanzu ba a ga yara uku ba, inda ya ƙara da cewa masu iyo na cikin gida sun ceto wasu daga cikin wadanda abin ya shafa.
Har yanzu gwamnatin jihar Neja ba ta mayar da martani kan lamarin ba. Kiraye-kirayen da aka yi wa jami’in hulda da jama’a na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja, ba a ɗauka ba har ya zuwa ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Mutum 15 Sun Mutu a Hatsarin Jirgin Ruwa
A wani labarin kuma, mutum 15 sun rasa rayukansu bayan jirgin ruwan da suke ciki ya nutse a jihar Adamawa.
Hatstin ya auku ne bayan jirgin ruwan ya kife ne a tafkin Njuwa kusa da ƙauyen Dandu, ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng