Shugaba Tinubu Ya Amince Da Sabbin Shugabannin 2 a Ma'aikatar Kiwon Lafiya

Shugaba Tinubu Ya Amince Da Sabbin Shugabannin 2 a Ma'aikatar Kiwon Lafiya

  • An yi sauye-sauye a ma'aikatar ilimi yayin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabbin nade-nade guda biyu
  • Sabbin nade-naden sun kasance a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) da hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIA)
  • An bukaci wadanda aka nada da su ba da fifiko wajen tabbatar da inganci, adalci da gaskiya yayin samar da kiwon lafiya mai kyau ga dukkanin al'ummar Najeriya

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin shugabanni biyu domin jagorantar hukumomi a ma'aikatar kiwon lafiya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, ya saki a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

Tinubu ya amince da nadin shugabannin NPHCDAN Da NHIA
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Sabbin Shugabannin Hukumomin NPHCDAN Da NHIA Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sabbin shugabannin da aka nada sune Dr Muyi Aina, shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) da Dr Kelechi Ohiri, shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIA).

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Amince Da Nadin Sabon Mai Binciken Kudi Na Kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takaitaccen tarihin sabbin shugabannin

Dr. Muyi Aina, mutum ne mai kima a bangaren kiwon lafiya, ya yi digirgir a fannin kiwon lafiya daga jami’ar Harvard da kuma digiri na uku a jami’ar Johns Hopkins. Ya fara samun takardar shaidar aikin likita a jami'ar Ilorin.

Dr Kelechi Ohiri, wanda a baya ya taba rike mukamin Manajan Darakta a kungiyar 'Global Alliance for Vaccines' a Geneva, Switzerland, ya mallaki digiri na biyu a bangaren kiwon lafiya daga Jami'ar Harvard da digirgir na biyu a fannin manufofin jama'a daga Makarantar Gwamnati ta Harvard's Kennedy.

Ya fara aikin likitanci a Jami'ar Legas kuma ya sami gogewa sosai a Bankin Duniya da kamdanin McKinsey & Company, yana ba da gudummawar yin gyare-gyare a Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Birtaniya (NHS).

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga sabbin shugabannin wadannan hukumomi masu muhimmanci da su ba da fifiko wajen tabbatar da inganci, adalci da rikon amana yayin isar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga kowane bangare na al’ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Abun Murna Yayin da Tinubu Ya Amince Da Biyan Malaman ASUU Albashinsu Da Aka Rike

Tinubu ya dakatar da bude jami'o'i 37 da Buhari ya amince da kafa su

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a jinkirta fara aikin sabbin jami'o'i da gwamnatin da ta gabata ta tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da kafa su.

Tahir Mamman, ministan ilimi ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, a babban birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng