Lamunin Karatu: Ilimi Ake Son Hana Matasa, Ya Kamata Su Yi Zanga-Zangar Adawa Da Shirin, Dr Sule

Lamunin Karatu: Ilimi Ake Son Hana Matasa, Ya Kamata Su Yi Zanga-Zangar Adawa Da Shirin, Dr Sule

  • Tun bayan kawo tsarin lamunin karatu, dalibai su ke zuba ido don ganin an fara shirin
  • Sai dai wasu na ganin kaman an fada ne babu ranar aiwatarwa saboda yadda lamura su ke a kasar
  • Legit Hausa ta tattauna da wani malamin Jami’a mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum inda ya fede komai

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da bai wa dalibai lamunin karatu don inganta harkar ilimi tare da saukaka wa marasa galihu damar yin karatu a kasar.

Dalibai da dama sun yaba wa wannan tsari na ba da lamunin karatun da Tinubu ya kawo wanda su ke ganin za su samu damar yin karatu a cikin sauki.

Menene bashin karatun dalibai na Tinubu ke nufi a dalibai
Bayani kan Bashin karatu da Tinubu ya kawo. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Menene masanin ke cewa kan lamunin dalibai?

Wakilin Legit Hausa ya tattauna da wani mai fashin baki a harkokin yau da kullum kuma malamin Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe, Dakta Babayo Sule.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Shiga Hannu Kan Zargin Yunkurin Kisan Almajiri Bayan Malaminsu Ya Lalata Neman Aurensa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Sule ya ce wannan tsari kamata ya yi daliban su yi zanga-zanga kada a kawo shi, idan da sun san abin da ke kunshe a cikinsa.

Ya ce babu wani muhimmanci da tsarin ke da shi illa kawai shiri ne na ‘yan jari hujja don gurgunta ilimi da hana ‘ya’yan talakawa karatu.

A cewarsa:

“Maganar lamuni ba sabon abu ba ne a Najeriya, an taba yin ‘Student Loan Board’ a shekarar 1980 amma bai yi nasara ba aka watsar da shi, a fahimta ta wannan ba abin murna ba ne ga dalibai.
“Yanzu kusan dan Najeriya kyauta ya ke karatun gaba da sakandare, an yi kiyasi gwamnati na kashe wa kowane dalibi miliyan uku da rabi kafin gama digiri, abin da yanzu ta ke son yi shi ne kaman ta gaji da biyan kudin makaranta.

Kara karanta wannan

Duniya Ta Yi Tir da Israila a Kan Kashe Fiye da Bayin Allah 500 Kwance a Asibiti

“Daliban sun dauka cewa za a dumbulo kudi a ba su, ba haka ba ne kudin da za a bayar gaba daya a kudin makaranta zai kare, idan ka gama za ka zo ka cigaba da biya wanda kasashen duniya da dama ke yi.

Ya ce ka’idojin samun lamunin ma suna da wuyan sha’ani, wanda samun garanto ma matsala ne tun da duk dalibin da bai biya bashin ba, na kan wanda ya tsaya masa domin karbar lamunin.

Wace shawara ya bai wa daibai kan shirin lamunin?

Ya kara da cewa:

“Tabbas za a yi wanna tsari tun da har majalisa ta tabbatar da shi a matsayin doka, saboda gwamnati ce ta ‘yan jari hujja wanda su ka koya a wurin gwamnatocin kasashen duniya, babu makawa za a yi wannan tsarin lamunin karatu.”

Da wakilin Legit Hausa ya tambaye shi ko hakan na nufin an lasa wa dalibai zuma a baki ne, sai Daktan ya ce:

Kara karanta wannan

Masanan Duniya Sun Taimaki Tinubu da Muhimman Shawarwari da $1 ta Zarce N1000

“Babu wani batun lasa zuma a baki, da daliban sun fahimci tsarin, ya kamata su yi zanga-zanga na kin amincewa da shi, domin karatu ake son hana su yi, misali, ka yi karatun bashi shekara nawa za ka yi kana biyan wadannan kudaden.
“Ni banga muhimmancin wannan tsari ba in har don talakawa ake yi, meye muhimmanci gwamnati a yanzu? Ta cire tallafin mai, ta cire a lantarki, babu ruwan sha, babu tsaro, yanzu kuma za a cire a ilimi.”

Tinubu ya kawo tsarin bai wa dalibai lamunin karatu

A baya kun ji cewa Shugaba Tinubu ya shirya bai wa dalibai lamunin karatun musamman ‘ya’yan talakawa.

Shugaban ya shirya kawo tsarin ne don bai dalibai damar samun karatu cikin sauki a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.