Gwamna Radda Na Katsina Ya Bukaci Bai Wa Mutane Damar Siyan Bindiga Kamar ’Yan Bindiga
- Gwamna Dikko Radda na Katsina ya bukaci bai wa mutane damar siyan makamai kamar yadda ‘yan bindiga ke yi
- Radda ya ce ana kiransu gwamnoni ne kawai amma ba su da ikon komai a tsaro na umartan sojoji ko jami’an 'yan sanda
- Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Juma’a 20 ga watan Oktoba a Abuja yayin ganawa da manema labarai
Jihar Katsina – Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya ce ya kamata a bai wa mutanr damar siyan bindiga da sauran makamai kamar yadda ‘yan bindiga ke yi.
Radda ya ce ‘yan bindiga na siyan makamai ba tare da tarnaki ba a kasuwanni ya kamata mutane ma su samu wannan damar don kare kansu, Daily Trust ta tattaro.
Meye Gwamna Radda na Katsina ya ce kan rike makamai?
Gwamnan ya bayyana haka yayin hira da manema labarai a Abuja a yau Juma’a 20 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce mutane su bar ganin laifin gwamnoni a jihohin da ake fama da rashin tsaro inda ya ce kawai su ne shugabanni amma ba su da damar umartan ‘yan sanda da sojoji.
A cewarsa:
“Mu kawai ana kiranmu gwamnoni ne masu tsaron jihohi amma ba mu da ikon umartan jami’an soji ko ‘yan sanda saboda su na karbar umarni daga sama.
“A kokarin mu na kawo karshen tsaro, mun samar da kwamitin tsaro na CWC don taimakawa a dakile matsalar tsaron da mu ke fama da shi.
“Akwai sarakunan gargajiya da su ke ciki wasu kuma muna kan bincikensu, don haka babu wanda za mu bari da mu ka samu da laifi.”
Wane martani Radda na Katsina ya yi kan sulhu da 'yan bindiga?
Gwamnan ya ce babu maganar tattaunawa da ‘yan bindigan a tsarinsa, amma ya ce idan su ka bukaci ajiye makami da kansu, akwai yiyuwar karbar su da dawo da su cikin al’umma.
Ya kara da cewa:
“Idan har dan bindiga zai shiga kasuwa ya sayi bindigar AK-47 da sauran makamai, ya kamata mutane a barsu su siya don kare kansu.”
Radda ya ce ba zai nade hannu ba ya na ganin ana hallaka bayin Allah saboda rashin makamai masu kyau, Daily Post ta tattaro.
'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban karamar hukuma a Kebbi
A wani labarin, masu garkuwa sun sace tsohon shugaban karamar hukumar Ngeski da ke jihar Kebbi.
Maharan bayan sace Hassan Garba sun kuma sace wasu mutane 12 a hanyar Tegina zuwa Kontagora a jihar Neja
Asali: Legit.ng