Fasto Ayodele Ya Bukaci Tinubu Ya Kama Sheikh Gumi Saboda Kalamansa Kan Wike
- Shahararren Fasto Elijah Ayodele ya gargadi Sheikh Ahmed Gumi kan ta da rikicin addini a Najeriya
- Ayodele ya ce Gumi na amfani da Wike don kawo rikicin addini a Najeriya inda ya bukaci Tinubu ya kama shi
- Faston ya gargadi Gumi da ya tsame Kiristoci a cikin zancensa inda ya ce malamin ba shi da bambanci da Taliban
FCT, Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele ya kirayi a kama Sheikh Ahmed Gumi saboda kalamansa kan Kiristoci.
Ayodele na magana kan martani da Gumi ya yi kan ministan Abuja, Nyesom Wike bisa ga zargin kiyayyarsa ga addinin Musulunci.
Meye Gumi ya ce kan Wike da ya jawo martanin Fasto?
Gumi a jiya Alhamis 19 ga watan Oktoba ya bayyana Wike a matsayin shaidanin mutum inda ya ce bai kamata a aminta da Kiristoci a harkar tsaro ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani, malamin ya bukaci a cire Wike a matsayin minista tare da maye gurbinshi da Musulmi, Tribune ta tattaro.
A martaninshi, Ayodele ya ambaci Gumi da shaidan wanda ya zo don tarwatsa zaman lafiyar Najeriya.
Faston ya gargadi Gumi da tsame sunan Kiristoci a cikin zancen inda ya ce ya bar Wike ya yi aikinsa tun da ba iya Musulmai abin zai shafa ba.
Meye Faston ya bukaci Tinubu ya yi kan Gumi?
Ya ce:
"Gumi ya kamata ya bar maganar Kiristoci, ya yi magana akan addininsa, ya zo ne ya tarwatsa Najeriya wanda dole gwamnati ta yi hankali da shi.
"Babu bambanci tsakanin Gumi da Taliban ya kamata Tinubu ya dauki mataki a kan shi bai kamata ya yi amfani da Wike wurin tayar da rikicin addini ba."
Faston ya bukaci a dauki Sheikh Gumi zuwa asibiti don gwajin kwakwalwarsa dangane da abubuwan da ya ke fada, Newstral ta tattaro.
Gumi ya ambaci Wike da shaidan, ya bukaci a cire shi a minista
Kun ji cewa, sharararren malami Sheikh Gumi ya bukaci Tinubu ya cire Wike a mukamin minista tare da sauya shi da Musulmi.
Gumi ya kira Wike da shaidan inda ya ce zai wahala gwamnatin ta dore da irinsu a Wike a cikinta.
Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Wike da shirin rushe bangaren masallacin Abuja.
Asali: Legit.ng