Tinubu Ya Fara Sabon Yunkuri Domin Hana FBI Fallasa Ragowar Sirrinsa a Amurka
- Bola Ahmed Tinubu ya na cigaba da fuskantar barazana a kan kujerar shugaban Najeriya daga wajen Alhaji Atiku Abubakar
- Wazirin Adamawa ya ce shugaban kasar ya na neman yadda zai hana jami’an FBI su fitar da rahoton da ake nema a kan shi
- An bukaci hukumomin Amurka su fitar da rahoton shari’ar kwayoyi da aka yi da Tinubu a Illinois shekaru 30 da su ka wuce
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya na kokarin ganin ya hana hukumomi shida da ke kasar Amurka fitar da wani tsohon rahoto a game da shi.
Sun ta ce ana shirin sakin cikakken bayanin abin da ya faru a shari’ar da aka yi da Bola Ahmed Tinubu a wata kotu a Illnos a shekarar 1993.
A wancan lokaci, shugaban Najerya na yau ya sallama wasu $460, 000 da ya mallaka bayan bincike da aka yi kan harkokin safarar kwayoyi.
Alakar Bola Tinubu da harkar kwayoyi
Ana zargin kudin da Adegboyega Akande da Abiodun Agbele su ka samu ta hanyar cinikin miyagun kwayoyi sun shiga asusun Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin haka ne shugaban kamfanin PlainSite, Aaron Greenspan da wani ‘dan jarida, David Hundeyin su ka nemi jin gaskiyar abin da ya faru.
Jaridar ta ce Hundeyin da Greenspan sun yi karar FBI, CIA, DEA, IRS da sakataren gwamnati domin samun duk bayanan hukuncin kotun.
Masu shigar da karar sun kafa hujja da dokar samun bayanai ta FOI, kuma kotu ta yi hukuncin cewa lallai a biya masu bukatun da su ka nema.
Rahoton shari'ar Tinubu zai fito
Zuwa watan Oktoban nan na 2023 ake sa ran za a saki rahoto mai dauke da shafuka 300 da su ka yi bayanin abubuwan da su ka faru a 1993.
Idan hakan ba ta samu ba, za a rika fitar da shafuka 450 na tsawon makonni shida har a samu cikakken rahoto na hukuncin kotun da aka yi.
Atiku ya tsokano Shugaba Tinubu
The Cable ta ce Atiku Abubakar ya yi magana ta bakin hadiminsa, ya na cewa shugaban ya na neman hanyar da za a rufa masa asirinsa.
Bayanan binciken da ake nema sun kai shafuka 70, 000 amma za a takaita a kan 2, 500, watakila hakan ba zai yi wa Bola Tinubu da APC dadi ba.
Tinubu ya saba yin mai ya lashe
Ku na da labari matasa irinsu Maryam Shetty da Imam Kashim Imam sun ga samu da rashi lokaci daya bayan fasa ba su mukamai a gwamnati.
An zargi Kashim Shettima, Godswill Akpabio, Femi Gbajabiamila, Nuhu Ribadu da yakar Nasir El-Rufai a zama minista a gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng