Wike Ya Ba da Wa’adin Sa’o’i 24 Ga Hukumar FCDA Don Samo Tsarin Biyan Diyyar Masallacin Abuja
- Ana ci gaba da cece-kuce kan kokarin rushe wani bangaren babban masallacin Abuja da minista Wike ke shirin yi
- A halin yanzu ministan ya bukaci sakataren Hukumar FCDA, Injiniya Shehu ya kawo masa bayani kan matsayar masallacin
- Ministan ya bukaci hakan ne don sanin irin tsarin da za a bi na biyan kudin diyya ga kwamitin masallacin na Abuja
FCT, Abuja – Minsitan Abuja, Nyesom Wike ya bai wa sakataren hukumar FCDA wa’adin sa’o’i 24 don yin bayanai kan matsayar babban masallacin Abuja.
Wike ya bukaci hakan ne daga sakataren, Injiniya Shehu Ahmed don sanin wurin da masallacin ya ke da kuma tsarin kudin diyya da za a biya.
Meye Wike ke shirin yi kan masallacin Abuja?
Hausa Legit ta tattaro cewa aikin fadada hanya a yankin zai shafi wani bangaren babban masallacin da ke birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista ya ba da wannan umarni ne yayin karbar bakwancin kwamitin gudanarwa na masallacin wanda Mai Martaba Etsu Nupe, Yahaya Abubakar ya jagoranta.
Mai Martaban ya bukaci ministan ya bai wa kawamitin karin lokaci don fadada filaye da hukumar FCDA ta ba su.
Ya kuma roki ministan da ya ba da na shi gudumawa don ganin an karasa aikin gyaran masallacin da ya dauki lokaci ana yi, cewar Daily Trust.
A martaninshi, Wike ya karyata jita-jitar cewa ya na adawa da Musulunci inda ya ce wannan aikin ‘yan adawa ne kawai.
Ya ce:
“Bari in fara daga abin aka fada min, cewa na umarci rushe babban masallacin Abuja, ina son ku sani cewa mutane su na amfani da abubuwa da yawa don kifar da abokin gabarsu.
“Sarkin Musulmi mutum ne wanda na ke mutuntashi matuka, ba kawai ina daukarshi a matsayin yaya na ba ne, a matsayin uba na ke kallonshi.
“Duk wani abu game da masallacin nan wanda shi ne shugaba zan ba shi hadin kai iya karfina.”
Wike ya ce duk wata gwamnati za ta so ta ba da gudumawa a irin wannan aiki musamman da aka ce Obasanjo shi ya kafa kwamitin neman taimakon gyaran masallacin, Trust Radio ta tattaro.
Wike ya bayyana cewa ba ya adawa da Musulunci
A wani labarin, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana matsayarsa kan shirin rushe bangaren babban masallacin Abuja.
Wike na magana ne bayan an zarge shi da kin jinin Musulunci inda ya ce ba ya adawa da Musulunci.
Asali: Legit.ng