Wike Shaidani Ne, Ba Zai Yi Wu a Bar Tsaron Najeriya Hannun Kirista Ba - Gumi

Wike Shaidani Ne, Ba Zai Yi Wu a Bar Tsaron Najeriya Hannun Kirista Ba - Gumi

  • Malamin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya yi zazzafan martani a kan gwamnatin Najeriya
  • Gumi ya bayyana ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a matsayin shaidanin mutum kan karbar bakuncin jakadan Isra'ila a Najeriya
  • Ya bayyana cewa idan har Shugaban kasa Tinubu bai sauke Wike ba, toh ba zai yi mulkin shekaru takwas ba

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a matsayin shaidanin mutum kan tarban ambasadan Isra’ila a Najeriya a ofishinsa.

Malamin addinin ya bayyana hakan ne a wani bidiyo mai tsawon mintuna 14 da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yayin da yake karantar da dalibansa.

Gumi ya bukaci Tinubu da ya tsige Wike daga matsayin ministan Abuja
Wike Shaidani Ne, Ba Zai Yi Wu a Bar Tsaron Najeriya Hannun Kirista Ba - Gumi Hoto: @TheoAbuAgada/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Tinubu ba zai yi shekaru takwas ba idan bai sauke Wike ba - Gumi

A cikin wa'azinsa, Gumi ya kuma tabbatar da cewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai yi mulki na shekaru takwas ba idan har bai tsige Wike daga matsayin ministan Abuja ba.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Zazzafan Martani Yayin da Sheikh Gumi Ya Kira Wike Da "Shaidanin Mutum"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar malamin addinin, yana da matukar hatsari mika ragamar tsaron kasar nan a hannun kiristoci da yan kudu.

Malamin addinin ya ce Musulman da aka nada a manyan mukaman tsaro duk suna ne amma ba su ke kula da ragamar rundunar sojoji da juya ta ba.

Ya kuma bayyana wadanda suka yi kamfen din tikitin Musulmi da Musulmi a matsayin munafukai mayun kudi wadanda ke bibiyar daloli don jin dadi da son duniya.

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

"Minista na Abuja wannan shaidanin mutum, dama tun da aka sa shi ba ina gaya maku shaidani bane, wasu na wani magana. Ya je ya kira ambasadan wai Isra'il, wai aka ce wani yake turowa ban gani ba amma ban san ko ya tabbata ba. Amma dai abun da ya tabbata ya ce zai kira Isra'il su zo su saka tsaro a cikin garin Abuja, Saboda haka Abuja za ta koma kamar Tel Aviv, idan an ga irinmu masu gemu a ce billahi a kashe shi.

Kara karanta wannan

Ba Za Ayi 8 ba: Gumi Ya 'Tona Asirin' Gwamnatin APC, Ya Nuna Tinubu ba Zai Zarce ba

"Ina masu tikitin Musulmi da Musulmi? Munafukan mutane, munafukan banza. Abuja ta koma Tel Aviv domin tsaron kasa shine mutane. Ba ku ji sun yi tsit ba? Sun san abun da suke yi, kuma yanzu abun da suke yi, wallahi wani shugaban Miyyeti Allah ya zo yake gaya mun wai an zo an gaya masa cewa in an kiraka maganar sulhu da mutanen nan na daji kada ka shigo kar ka yi, ka bar shi.
"Dama take-take ne, shugabanninmu musulmai sune shugaban tsaro amma wani irin shugabanci ne ainahin mai bindigar mai rikawa mai halbawa sune? ba mu bane, wayo ne ake yi mana, akwai ajanda. Amma suna wayo da hankalinmu mu dukka, ba me fahimta, basira ana mana wayo."

Ga cikakken bidiyon a kasa:

Juyin mulki: Dakta Gumi ya ce wurin Tinubu ya kamata malamai da sarakuna su fara zuwa ba Nijar ba

A wani labari na daban, fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya tofa albarkacin bakinsa dangane da ziyarar da malamai, sarakuna da wakilan ECOWAS suka kai Nijar.

Ya ce fadar shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kamata su je domin neman sulhu ba jamhuriyar Nijar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng