Gobara Ta Yi Ajalin Mutane 2 a Gidan Mai Tare da Raunata Wasu a Jihar Ogun

Gobara Ta Yi Ajalin Mutane 2 a Gidan Mai Tare da Raunata Wasu a Jihar Ogun

  • Gobara ta yi ajalin mutane biyu a jihar Ogun bayan wani gidan mai ya kama da wuta a jiya Laraba
  • Lamarin ya faru ne a wani gidan mai da ake kira ‘Nine Energy’ wanda ke yankin Asero da ke birnin Abeokuta
  • Kakakin ‘yan sanda a jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin a jiya Laraba 18 ga watan Oktoba

Jihar Ogun– Akalla mutane biyu ne su ka mutu bayan wuta ta kama a wani gidan mai a Asero da ke Abeokuta cikin jihar Ogun.

Lamarin ya faru ne a jiya Laraba 18 ga watan Oktoba a wani gidan mai da ake kira ‘Nine Energy’a jihar.

Mutane biyu sun mutu yayin gobarar gidan mai a Ondo
Iftila'in Gobara Ta Yi Ajalin Mutane 2 a Gidan Mai. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Meye ya jawo gobaran a gidan mai na Ogun?

Daily Trust ta tattaro cewa gobarar ta kama ne bayan wata tanka na zuba bakin mai ga wata tanka a gidan mai din.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mutane Sama da 35 Sun Mutu Yayin da Wasu Akalla 40 Suka Jikkata a Hatsari a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar cewa wadanda su ka rasa rayukansu a iftila’in sun hada da direban motar da kuma yaronsa wanda su ka zo karbar bakin mai din.

Jami’an kasha gobara ta jihar sun yi gaggawar zuwa wurin da alamarin ya faru inda su ka tarar har motar ta kone.

Sannan jami’an ‘yan sanda da ta hukumar tsaro ta NSCDC sun samu halartar wurin don ba da taimakon da ba za a rasa ba na dakile rasa rayuka da dukiyoyi.

Wane martani 'yan sanda su ka yi kan gobarar a Ogun?

Wata majiya ta tabbatar da cewa gobarar ta fara da misalin karfe 10 na safe bayan fara juyen bakin man.

Majiyar ta ce:

“Kawai ganin bakin hayaki mu ka yi a sama na fita daga gidan mai din, babu wanda ya iya zuwa kusa da gidan saboda karfin wutar gobarar.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Bindige Wani Shahararren Dan Kasuwa a Arewa Bayan Ya Musu Tirjiya, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

“Daga baya mun fahimci cewa wutar ta fara ne yayin juyen bakin da ake daga wata tanka zuwa wata inda daya tankar ta kama da wuta.
“Dukkan mutane biyun da ke cikin tankar da ke karbar bakin mai din sun rasa rayukansu “

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin sai dai ta ce ba ta san mutane nawa abin ya shafa ba, cewar Vanguard.

'Yan sanda sun kama matashi kan zargin kashe mahaifinsa

A wani labarin, Rundunar 'yan sanda a jihar Ogun ta cafke matashi kan zargin kisan mahaifinsa a Ogun.

Matashin mai suna Ridwan ya shiga hannu ne bayan kama shi dumu-dumu kan kisan don kudin asiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.