NSIPA: Yadda Za Mu bi Wajen Rabawa Talakawa da Marasa Karfi Kudi Inji Gwamnati

NSIPA: Yadda Za Mu bi Wajen Rabawa Talakawa da Marasa Karfi Kudi Inji Gwamnati

  • Shugabar hukumar nan ta NSIPA ta yi bayanin tsarin aikinsu a lokacin da ake tantance ta a majalisar dattawan Najeriya
  • Halima Shehu ta shaidawa Sanatoci cewa akwai talakawan da ke karkashin tsarinsu wanda za a rika aika masu N5000
  • Baya ga tsarin CCT, gwamnatin tarayya za ta bada horo kuma ta taimakawa kananan ‘yan kasuwa da jari na N150, 000

Abuja - Shugabar hukumar NSIPA da ka fito da ita domin marasa karfi, Halima Shehu ta yi bayanin yadda za su taimakawa masu rauni.

A jiya Premium Times ta rahoto Halima Shehu ta na cewa gwamnatin tarayya za ta raba N5, 000 ga talakawa da nufin a rage talauci.

Akwai rukunin wadanda gwamnatin Najeriya za ta raba masu N150, 000 domin su fara kanana da matsakaitan kasuwanci a kasar.

Kara karanta wannan

Damfara: Kotu Ta Tisa Keyar Malam Gambo Zuwa Gidan Yari Akan Daura Auren Surukarsa Da Buhari

Shugabannin Najeriya
Shugabannin Najeriya za su taimakawa talakawa Hoto:The Senate President - Nigeria
Asali: Facebook

Za a taimakawa kasuwanci

Kafin kai ga bada wadannan kudi, shugabar NSIP ta ce sai an ba ‘dan kasuwa horo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabar hukumar ta yi wadannan bayanai a lokacin da ta bayyana gaban Sanatoci domin majalisar dattawa ta tabbatar da nadinta.

Yayin da za a rika raba N5000 ga marasa halin a duk wata, shi kuwa jarin sau daya za a bada shi ga wadanda su ka kware a kasuwanci.

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce za a shafe shekaru uku ana yin rabon kudin, ana sa ran zuwa wannan lokaci talaucin ya ragu.

CCT: Gwamnati ta hada kai da bankin Duniya

A tsarin CCT, Misis Halima Shehu ta ce za su aika kudin ka-tsaye ne daga bankin CBN zuwa asusun wadanda za su amfana da kudin.

Har ayi a gama, hukumar NSPIA na sa ran kudin da za a raba ba za su shigo hannunta ba, wannan ne zai tsarin ya yi tasiri sosai.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mutane Sama da 35 Sun Mutu Yayin da Wasu Akalla 40 Suka Jikkata a Hatsari a Arewa

Bankin duniya da sauran manya da ake ji da su za su sa ido domin tabbatar da cewa an yi gaskiya, kudin ba su koma aljihun 'yan tsiraru ba.

Dala ta kufcewa Tinubu

Jama’a sun fara tunanin anya a haka Gwamnatin Bola Tinubu za ta farfado da tattalin arziki ganin yadda Dala ta haura N1, 100 a yanzu.

‘Yan kasuwa su na kukan cewa karancin kudin kasashen wajen ne yake jawo tashin na su bayan an kawo wasu sababbin tsare-tsare a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng