Tinubu Ya Dakatar Da Bude Jami'o'i 37 Da Buhari Ya Amince Da Kafa Su
- Gwamnatin Shugaban kasa Tinubu a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, ta dakatar da fara aikin sabbin jami'o'i 37
- Gwamnatin da ta gabata ta tsohon shugaban Muhammadu Buhari ce ta amince da kafa jami'o'in tana gab da mika mulki
- Tinubu ya ce an dauki matakin ne bisa la’akari da bukatar samar da kudade da ingantattun shirye-shirye na ilimi ga wadannan jami’o’in.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a jinkirta fara aikin sabbin jami'o'i da gwamnatin da ta gabata ta tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da kafa su.
Ministan Ilimi, Tahir Mamman ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, a babban birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.
Dalilin dakatar da bude jami'o'i 37 da Buhari ya amince da su
Katsina: Bayan Kafa Rundunar Tsaro, Gwamnatin Radɗa Ta Yi Magana Kan Yiwuwar Tattaunawa da 'Yan Bindiga
Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rahoto, Mamman ya ce hakan ya kasance ne bisa la’akari da kudaden da ake bukata don samar da ingantattun shirye-shirye na ilimi ga wadannan jami’o’in.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Buhari ta amince da ba da lasisi ga sabbin jami’o’in 37 a kasar yan kwanaki kafin ya mika mulki ga sabuwar gwamnati.
Mamman ya ce:
"Gwamnatin da ta shude ta amince da yawancin wadannan sabbin jami'o'in ne a karshen mulkinta. Bayan tarin nazari, Shugaban kasa Tinubu ya ga cewa ya kamata a dan dakata da bude su.
“Hakan ba wai yana nufin za a soke jami’o’in ba ne, illa dai a duba su ta fuskar karfinsu da alfanun da daliban za su samu.
"Abin da sabuwar gwamnati za ta mayar da hankali a kai ta bangaren ilimi shi ne kan horon da irin wadannan jami'o'i za su bai wa matasa.
"Muna fatan jami'a inda dalibai za su iya kammala karatu da fasahar da ba wai su kadai zai amfana ba harma ga ci gaban tattalin arzikin kasar."
Ministan ya bayyana cewa gwamnati na duba irin kalubalen da jihohi ke fama da su na rashin samun kudaden Hukumar Ilimi ta bai daya.
Ya ce shugaban kasar ya amince da sake nazari kan kudaden don ba da jihohin damar samunsu cikin gaggawa.
Hukumar NUC ta musanta cire bambancin da ke tsakanin kwalin digiri da HND
A wani labarin, mun ji cewa hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa (NUC) ta ce har yanzu akwai banbance-banbancen da ke tsakanin masu digiri na jami’a da masu kwalin babbar Diploma ta ƙasa (HND).
Hukumar ta ƙara da cewa har yanzu Tinubu bai sanya hannu kan dokar soke bambancin ba.
Asali: Legit.ng