Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Babban Dan Kasuwa a Jihar Neja Bayan Yi Musu Tirjiya

Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Babban Dan Kasuwa a Jihar Neja Bayan Yi Musu Tirjiya

  • Ana cikin jimami bayan maharan sun hallaka wani dan kasuwa a jihar Neja yayin da su ka afka masa a cikin shagonsa
  • Marigayin mai suna Alhaji Samiu Jimoh ya gamu da tsautsayin ne bayan maharani sun yi kokarin tafiya da shi amma ya ki
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata

Jihar Neja – ‘Yan bindiga sun yi ajalin wani shahararren dan kasuwa Alhaji Abdul-Samiu Jimoh a karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja.

Daily Trust ta tattaro cewa marigayin ya rasa ransa ne bayan maharan sun kai masa hari a shagonsa da misalin karfe takwas na ranar Talata da ta gabata.

Masu garkuwa sun yi ajalin wani dan kasuwa a Neja
Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Dan Kasuwa a Neja. Hoto: Umar Bago.
Asali: Facebook

Meye ya jawo kashe dan kasuwar a Neja?

Majiyar ta tabbatar da cewa marigayin ya ki bin umarnin maharani ne na tafiya da shi wanda hakan ya yi sanadin rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Abin Tausayi: 'Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Mataimakin Magatakardar Kwalejin Gwamnatin Tarayya, An Bazama Nemansu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin, Idris Mohammed ya bayyana cewa dan kasuwar ya ki amincewa da su maharan su tafi da shi wanda ya sa su ka harbe shi.

Ya ce:

“Maharan sun harbi dan kasuwar ne bayan ya ki bin umarninsu na tafiya da shi inda su ka ce ma sa ya biyo su, a yayin cece-kucen ne su ka harbe shi.”

Wane martani 'yan sanda su ka yi a Neja?

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an kashe dan kasuwar ne a shagonsa na siyar da kayan mota.

Ya ce:

“A ranar 10 ga watan Oktoba da misalin karfe 9:45 na dare mun samu rahoton cewa ‘yan fashi da masu garkuwa sun kai hari shagon Alhaji Samiu Jimoh a shagonsa da ke kan hanyar Bida a Mokwa.”

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Gidan Ɗan Majalisar Arewa, Sun Tafi da Matarsa da 'Ya'yansa

Ya kara da cewa kafin zuwan jami’an ‘yan sanda wurin da lamarin ya faru, tuni har sun harbe dan kasuwar.

Abiodun ya ce sun kwashi dan kasuwar zuwa babban asibitin Mokwa inda daga nan ne aka tabbatar da cewa ya mutu.

Wannan na zuwa ne bayan 'yan bindiga sun hallaka wasu mutum 12 da su ke aiki a wurin ma'adinai a kwanakin baya, cewar Channels TV.

‘Yan bindiga sun hallaka tsohon soja a Imo

A wani labarin, ‘yan bindiga sun yi ajalin wani tsohon soja kuma mataimakin magatardar Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke jihar Ebonyi.

Marigayin mai suna Innocent Obi ya gamu da ajalinsa ne yayin da maharan su ka kai masa hari a gidansa da ke jihar Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.