Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 3 da Sace Hakimi a Jihar Zamfara
- Ƴan bindiga sun kai wanu mummunan farmaki a ƙauyen Bagega da ke ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara
- Migayun ƴan bindiga sun halaka mutum uku tare da raunata wasu mutane da dama a yayin harin da suka kai
- Haka kuma sun yi garkuwa da Hakimin ƙauyen, ƴarsa da wasu tarin mutane masu yawa a mummunan harin
Jihar Zamfara - Aƙalla mutum uku ne suka mutu sannan wasu 11 suka jikkata a wani hari da wasu ƴan bindiga suka kai a ƙauyen Bagega da ke ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara.
A yayin harin, ƴan bindigan sun yi awon gaba da hakimin ƙauyen, da ƴarsa mai shekara takwas da kuma wasu kimanin mutum 10, cewar rahoton TRT Afrika.
Wani mazaunin ƙauyen da ya tsere a lokacin harin mai suna Abdullahi Bagega, ya shaida wa Channels tv a ranar Laraba cewa, ƴan bindigan sun mamaye ƙauyen ne a kan babura a yammacin ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba.
Yadda ƴan bindigan suka kawo harin
Abdullahi ya yi nuni da cewa ƴan bindigan na isowa suka fara harbe-harben bindiga, wanda hakan ya tilasta wa mazauna ƙauyen guduwa domin tsira da rayukansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an kashe mutum uku, wasu mutum 11 kuma sun samu munanan raunuka, inda ake ba su kulawa a asibitoci daban-daban.
Abdullahi ya ƙara da cewa har yanzu ba a ga wasu mazauna ƙauyen ba da suka gudu a lokacin harin.
A kalamansa:
"Sun yi garkuwa da Sarkin Gabas na ƙauyenmu da ƙaramar ƴarsa ƴar kimanin shekara takwas, wasu mutum shida da mutum huɗu daga wani ƙauye a kusa da Bagega. Adadin bai kai mutum 50 ba. Yanzu haka muna da mutum 11 da suka samu munanan raunuka."
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar bai tabbatar da aukuwar harin ba lokacin da aka tuntuɓesa, amma ya yi alƙawarin bayar da bayanai idan ya yi bincike domin sanin abin da ya auku.
An Halaka Diyar Dan Majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun sun aikaka kisan gilla kan ɗiyar wani ɗan majalisar dokokin jihar Borno a gidan mijinta.
Miyagun dai sun halaka marigayiyar ne bayan sun ɗaure mata hannayenta ta baya da ƙafafunta, sannan suka shaƙe ta har sai da ta daina numfashi.
Asali: Legit.ng