Ortom Ya Boye Asusu Sama Da 570, Ya Nuna Guda 25 Kadai, Gwamnatin Benue

Ortom Ya Boye Asusu Sama Da 570, Ya Nuna Guda 25 Kadai, Gwamnatin Benue

  • Gwamnatin jihar Benuwai ta bankaɗo badaƙalar yawan asusun bankin da Samuel Ortom ya ɓoye kafin ya bar mulki
  • Kwamishinan kuɗi da tsare-tsaren kasafi, Michael Oglegba, ya ce sun gano jihar tana da asusu sama da 600 amma 25 aka nuna wa sabon gwamna
  • Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Alia na APC ta gaji bashin kuɗi N359bn wanda ya kunshi basukan kananan hukumomi

Jihar Benue - Gwamnatin jihar Benue ta zargi tsohuwar gwamnatin da ta shude ta tsohon gwamna Samuel Ortom na PDP da yin amfani da asusu sama da 600.

Gwamnatin Benuwai karkashin Gwamna Hyacinth Alia na APC ta caccaki Ortom da ɓoye bayanan asusun banki sama da 570, inda ya nuna 25 kacal sa'ilin miƙa mulki.

Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom.
Ortom Ya Boye Asusu Sama da 570, Ya Nuna Guda 25 Kadai, Gwamnatin Benue Hoto: Samuel Ortom
Asali: UGC

Kwamishinan kuɗi da tsare-tsaren kasafin kuɗi na jihar, Michael Oglegba, ne ya faɗi haka yayin da tawagar ƙungiyar 'yan jarida (NUJ) ta kai masa ziyara a Ofis ranar Talata a Makurɗi.

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan Kafa Rundunar Tsaro, Gwamnatin Radɗa Ta Yi Magana Kan Yiwuwar Tattaunawa da 'Yan Bindiga

Ya ce bisa wannan dalili ne mai girma Gwamna Alia ya bada umarnin rufe dukkan asusun gwamnati bayan ya karɓi mulki, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gwamnatin Alia ta tono ragowar asusun

Kwamishinan kuɗi ya kara da bayanin cewa gwamnatin Ortom ta nuna wa Gwamna Alia asusu 25 ne kacal lokacin da ya karɓi ragamar mulki a watan Mayu.

Amma a cewarsa, bayanai daga hukumar kula da mu'amalar bankuna ta tarayya ya nuna gwamnatin Benuwai na da asusu sama da 600.

A jawabinsa ya ce:

"Lokacin da muka zo, mun nemi a bamu bayanan asusun banki kuma an gabatar mana da asusu 25. Da muka duba tsarin kula da mu'amalolin banki ya nuna jihar Benuwai tana da asusu sama da 600."
"Saboda haka ne gwamna ya ga ya kamata a rufe dukkan waɗan nan asusu domin gano me ke faruwa."

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP 5 Sun Sake Haɗe Kai, Sun Gana da Shugaba Tinubu a Villa, Bayanai Sun Fito

Oglegba ya jaddada cewa gwamnatin Alia ta gaji bashin N359bn wanda ya ƙunshi basukan da ake bin ƙananan hukumomin jihar, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Rikicin PDP: Gwamnonin G-5 Sun Sake Haduwa a Abuja, Sun Gana da Shugaba Tinubu

A wani rahoton kuma Gwamnonin G-5 na jam'iyyar PDP sun sake haɗa kansu, sun gana da shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Rahoto ya nuna tawagar G-5 wacce ta ƙunshi tsoffin gwamnoni 4 da gwamna mai ci, sun fara zama tsakaninsu a gidan Ministan Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262