Tinubu Ya Cigaba da Nadin Mukamai, An Nada Sabon CEO da Shugaban PTDF Ya Tafi

Tinubu Ya Cigaba da Nadin Mukamai, An Nada Sabon CEO da Shugaban PTDF Ya Tafi

  • Hukumar nan ta PTDF ta samu sabon shugaba bayan Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Ahmed Galadima Aminu
  • Ajuri Ngelale ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar a matsayinsa na Mai magana da yawun bakin shugaban kasa
  • Malam Ahmed Galadima Aminu ya san ciki da wajen PTDF kafin a ba shi wannan mukami, zai gama wa’adinsa ne a 2027

Abuja – Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Ahmed Galadima Aminu a matsayin sabon shugaban hukumar PTDF ta kasa.

A wani jawabi na musamman da ya fitar a ranar Talata, Ajuri Ngelale ya tabbatar da cewa Malam Ahmed Galadima Aminu zai jagoranci PTDF.

Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriyan ya ce shugaban ya na da wa’adin shekaru hudu, wanda za a iya ba shi damar zarcewa.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwan Sani Dangane da Sabon Shugaban Hukumar ICPC

Tinubu
Bola Tinubu ya nada Ahmed Galadima Aminu Shugaban PTDF Hoto: @Nosasemota
Asali: Twitter

Tashar Channels ta rahoto Ajuri Ngelale ya na cewa Bello Aliyu Gusau ya sauka daga kujerarsa, saboda haka sai aka nada sabon shugaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nadin sabon shugaban PTDF

"Sabon Babban Sakatare/CEO na PTDF bai dade da rike mukamin Babban Manajan sashen ilmi da horaswa na Hukumar ba.
Nadinsa ya biyo bayan murabus da Shugaba mai barin gado, Bello Aliyu Gusau ya yi domin ya tafi hutun ritaya na kwana 90 daga ranar 26 ga watan Satumba 2023.
Shugaban kasa ya umarci Ahmed Galadima Aminu ya hau kujerar rikon kwarya kafin ya fara wa’adinsa na shekaru hudu wanda zai zoma daga 26 ga watan Disamba 2023."

- Ajuri Ngelale

Kujerar shugaban Hukumar PTDF

A karshen jawabin, Daily Trust ta ce Bola Tinubu ya yi wa sabon shugaban fatan alheri, kafin nan ya yi nadin shugabanni a ICPC da NAHCON.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar ICPC

Kafin shi Legit Hausa ta fahimci irinsu Bello Aliyu Gusau, Muttaqa Rabe-Darma daga yankin Arewacin Najeriya sun rike wannan kujera a tarihi.

Mahaifin Bello Aliyu Gusau ya rike shugaban hafsun sojoji, ministan tsaro da mai bada shawara kan tsaro a gwamnatocin soja da farar hula.

"Tinubu na 3 ya zo a zaben 2023"

A jiya aka rahoto Babachir David Lawal wanda ya rike SGF a Najeriya ya ce jam'iyyar LP ta yi nasara a zaben shugaban kasa da aka yi, ba APC ba.

‘Dan siyasar ya yi ikirarin Peter Obi ya zo na daya, Atiku Abubakar na biyu sai Bola Tinubu, ya kuma ce shugaban Najeriyan bai da lafiya sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng