Shugaba Tinubu Ya Rubuta Wasika Ga Majalisa Wasika Kan Nadin Shugaban EFCC

Shugaba Tinubu Ya Rubuta Wasika Ga Majalisa Wasika Kan Nadin Shugaban EFCC

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da wasiƙa zuwa ga majalisar dattawa yana neman ta amince da naɗin Ola Olukoyede a matsayin shugaban EFCC
  • Shugaban majalisar dattawa, sanata Godswill Akpabio shi ne ya karanto wasiƙar a yayin zaman majalisar na ranar Talata, 17 ga watan Oktoba
  • Idan majalisar ta amince da naɗin Olukoyede, zai kasance shugaban hukumar na farko da ya fito daga yankin Kudancin Najeriya tun bayan da aka kafa ta

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rubutawa majalisar dattawa wasiƙa domin tantancewa tare da amincewa da naɗin Ola Olukoyede da Muhammad Hammajoda a matsayin shugaba da sakataren hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, shugaban majalisar dattawa, sanata Godswill Akpabio, ya karanta wasiƙar shugaban ƙasar a zauren majalisar, a ranar Talata, 17 ga watan Oktoban 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Rigima Ta Ɓalle a APC, Shugaban Majalisar Dattawa Ya Maida Martani Kan Zargin da Aka Masa

Tinubu ya bukaci majalisa ta amince da Olukoyede
Shugaba Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta amince da nadin Olukoyede
Asali: Twitter

A satin da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya sanar da naɗin Olukoyede a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC, bayan dakataccen shugabanta Abdulrasheed Bawa ya yi murabus.

Wanene Olukoyede sabon shugaban EFCC?

Olukoyede, fasto ne a Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), shi ne mutum na farko dan Kudancin Najeriya da zai rike muƙamin shugaban hukumar EFCC tun lokacin da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ta kafa hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An haife shi a ranar 14 ga Oktoba, 1969, Olukoyede ya fito ne daga Ikere-Ekiti, a jihar Ekiti, a yankin Kudu Yammacin Najeriya.

Sabon shugaban na EFCC ya kasance gogaggen lauya wanda ya shafe sama da shekaru 22 yana samun ƙwarewa a harkar binciken zamba, kula da bin doka da oda da bayanan kamfanoni.

Ya na da gogewa wajen tafiyar da hukumar EFCC domin a baya ya taba rike mukamin sakataren hukumar, da kuma shugaban ma’aikata na tsohon shugaban hukumar Ibrahim Magu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Zai Gabatar da Kasafin Kuɗin 2024 Wanda Ya Haura N20tr, Bayanai Sun Fito

Dalilin Ba Olukoyede Shugabancin EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sanya ya naɗa Ola Olukoyede matsayin sabon shugaban hukumar EFCC.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa ƙwarewar da Olukoyede ke da ita a hukumar ya sanya ya ba shi muƙamin shugabancinta, kuma naɗinsa bai saɓa doka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng