“Akwai Hatsari”: Yan Najeriya Sun Yi Tururuwan Zuba Diban Mai Daga Motar Tanka Da Ta Fadi a Hanya

“Akwai Hatsari”: Yan Najeriya Sun Yi Tururuwan Zuba Diban Mai Daga Motar Tanka Da Ta Fadi a Hanya

  • Wasu yan Najeriya sun jefa kansu a kasada yayin da suka taru don diban mai da ke kwarara daga wata motar tanka
  • Ba a tabbatar da ko abun da ke fita daga motar fetur bane, amma dai mutane da dama sun garzaya wajen don diban rabonsu
  • Wasu sun dauki hoton wajen mai cike da hatsari da wayoyinsu sannan suka wallafa shi a TikTok, inda aka samu mutumin miliyan 6.5 da suka kalla

Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuna yadda wasu yan Najeriya suka sanya kansu cikin kasada don diban man fetur da ke zuba a bakin hanya.

Wani bidiyo mai tsawon sakan 44 da @korasfiregrill ya wallafa ya nuna cewa wata motar tanka ta fadi a babban hanya sannan abun cikinta ya dungi kwarara.

Kara karanta wannan

“Na Tsorata”: Wani Dan Najeriya Ya Koka Yayin da Ya Ci Karo Da Wata Halitta a Janaretonsa, Ya Saki Bidiyo

Mutane na diban man fetur daga motar tanka
“Akwai Hatsari”: Yan Najeriya Sun Yi Tururuwan Zuba Diban Mai Daga Motar Tanka Da Ta Fadi a Hanya Hoto: TikTok/@korasfiregrill.
Asali: TikTok

Yayin da ba a fahimci ko fetur bane a ciki, mutane da dama sun yi tururuwan zuwa wajen da jarkoki iri-iri don diban rabonsu.

Da zaran sun isa wajen, sai bidiyon ya nuno suna diban man fetur da ke kwarara sai kace suna diban ruwa daga kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyo ya nuno yan Najeriya suna diban fetur da ke zuba daga motar tanka

A dan gaba kadan, ana iya ganin motar tankar da ta fadi tana zubo da mai inda ya dungi kwarara a titi.

Wani da ke wajen ya dauki bidiyon wajen mai cike da hatsari da wayarsa, yana bayanin yadda mazauna wajen ke taimakon junansu amma suka sanya kansu cikin hatsari.

Yan TikTok da dama da suka ga bidiyon sun ce idan har gobara ta barke a wajen ba karamin barna za ta yi ba.

Kara karanta wannan

“Yi Mun In Maka”: Wata Mata Ta Kashe Miliyoyi Wajen Siyawa Mijinta Kyaututtuka, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da TikTok sun yi martani

@israeloyime ya ce:

"Kai da kake daukar bidiyon ma baka son rayuwarka. Paparazzi da baya tsoron wuta.

@Culprint Quincy queues ta ce:

"Idan wani ya kunna karan sigari fa."

@Stanley Edmund ya ce:

"Me yasa mutane ke irin wannan barazana da ransu."

@Stereo ya ce:

"Mai daukar bidiyan a ganin shi ya tsira kuma babu ruwansa."

Wata mata ta fada ruwa tsudum yayin da dan achaba ya kutsa kai a ambaliyar ruwa, bidiyon ya yadu

A wani labarin na daban, wani bidiyo da ke nuna lokacin da wata mata ta fado daga babur sannan ta jike sharkaf da ruwan chabi a hanyar.

A cikin bidiyon da @jab0010 ya wallafa, alamu sun nuna matar na hanyarta ta zuwa wani muhimmin wuri ne lokacin da lamarin ya afku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng