An Tasa Keyar Matashi Zuwa Gidan Kaso Shekaru 10 a Kano Kan Safarar Tabar Wiwi

An Tasa Keyar Matashi Zuwa Gidan Kaso Shekaru 10 a Kano Kan Safarar Tabar Wiwi

  • Hukumar NDLEA a jihar Kano ta gurfanar da wani a gaban babbar kotun Tarayya kan zargin safarar tabar wiwi
  • Wanda ake zargin, Mohammed Sambo ya sha daurin shekaru 10 a gidan kaso wanda aka kama da wasu mutane bakwai
  • Kakakin hukumar a jihar, Sadiq Muhammad Maigatari ya tabbatar da hukuncin inda ya ce an samu busasshen tabar wiwi kilo 201 a motar Sambo

Jihar Kano - Babbar kotun Tarayya da ke Kano ta daure wani Mohammed Bako Sambo daurin shekaru 10 a gidan kaso kan zargin safarar kwayoyi da tabar wiwi.

Hukumar NDLEA a jihar Kano ta gurfanar da Sambo da wasu mutum bakwai a gaban Mai Shari'a, S. A Amobeda.

Ktu ta daure matashi shekaru 10 kan zargin safarar tabar wiwi a Kano
Hukumar NDLEA ta gurfanar da matashi a gaban kotu a jihar Kano. Hoto: NDLEA.
Asali: UGC

Meye NDLEA ke cewa kan kama matashin a Kano?

Kakakin hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari ya tabbatar da haka inda ya ce an daure Sambo har tsawon shekaru 10 a gidan kaso, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Bulala 15 Saboda Satar Rake

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Sambo ya kware wurin safarar miyagun kwayoyi daga jihar Ondo zuwa Arewacin Najeriya wanda aka kama a ranar 11 ga watan Nuwamba ta 2020.
"Jami'an NDLEA da ke sintiri a hanyar Kano zuwa Zaria sun yi arba da wata mota kirar Honda inda su ke zargin akwai wani abu, sun tsayar da motar inda ya ki tsayawa."

Me ye NDLEA ta samu a motar wanda ake zargin a Kano?

Ya kara da cewa:

"Sun bi motar har Unguwar Hotoro inda anan ne aka kama wanda ake zargin wanda aka samu tulin miyagun kayan maye a motar."

A yayin bincike an tabbatar da samun kilo 201 na ganyen wiwi a motar Sambo wanda daga bisani aka gane inda gidansa ya ke a Abuja a yankin Logokoma.

Wannan na zuwa ne bayan yawan sintiri da jami'an NDLEA ke yi a jihar ganin yadda shaye-shaye ke kara yawa a birnin, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu Ya Yi Bindiga da Naira Miliyan 400 a Kan Otel a Taron UN a Amurka

'Yan bindiga sun kai hari a kauyen jihar Kano

A wani labarin, wasu mahara sun kai farmaki a wani kauye da ake Yola a karamar hukumar Karaye da ke jihar Kano.

'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen wanda har yanzu ba a san yawan wadanda su ka rasa rayukansu ba yayin harin da ya tayar da hankula.

Wannan na zuwa ne bayan maharan sun kai hare-hare a kwanakin baya a kauyukan wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama yayin farmakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.