Gwamnati Ta Tsaida Lokacin da Za a Biya Ma’aikatan N-Power Bashin Albashin Wata 9

Gwamnati Ta Tsaida Lokacin da Za a Biya Ma’aikatan N-Power Bashin Albashin Wata 9

  • Akwai yiwuwar nan da ‘yan kwanaki kadan a ji gwamnatin tarayya ta far a jika hantar wadanda su ke aikin N-Power a kasar nan
  • Sanarwa ta fito cewa daga watan Nuwamba za a soma biyan albashin da aka dauki tsawon watanni tara ba a biya ma’aikata ba
  • Shugaban gudanarwa na shirin N-Power, Jamaluddeen Kabir ya yi bayanin hikimar dakatar da aikin, ya ce bincike ne ake yi

Abuja - gwamnatin tarayya ta ce ta shirya soma biyan duk bashin albashin da masu aikin N-Power su ke bi na tsawon wata da watanni.

A wani rahoto da mu ka samu a gidan rediyon Najeriya, an ji nan da ‘yan kwanaki kudin da ‘Yan N-Power su ke bi zai shigo hannunsu.

A lokacin da aka sanar da dakatar da wannan aiki, hankalin wasu matasan da su ka shafe wata da watanni ba tare da albashi ba ya tashi.

Kara karanta wannan

Duniya Ta Yi Tir da Israila a Kan Kashe Fiye da Bayin Allah 500 Kwance a Asibiti

Ministar jin kai, Betta Edu
Ministar jin kai, Betta Edu ta shiga lamarin N-Power Hoto: @NtemEngr
Asali: Twitter

Daga baya sai aka ji gwamnati ta yi karin-haske, ta yi alwashin nan gaba kadan za a biya duk wani ma’aikaci bashin kudin da ya ke bi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwar da aka samu ranar Litinin daga bakin shugaban sadarwa na kasa, Jamaluddeen Kabir, an tsaida lokacin biyan kudin.

Mista Jamaluddeen Kabir ya ce abin da ya sa aka dakatar da aikin shi ne domin a iya yin bincike kan duk matsalolin da ake fuskanta.

Babban jami’in yake cewa binciken ne zai bada damar gano abubuwan da ke ci wa wadanda su ke aikin na N-Power tuwo a kwarya.

Rahoton The Guardian ya ce a karshe gwamnati za ta samu damar da za ta yi wa tsarin garambawul bayan canjin gwamnati da aka samu.

Da yake bayani a kan batun albashin da su ka makale, Mr. Kabir ya ce kudin za su fara fitowa ne daga watan gobe watan Nuwamban 2023.

Kara karanta wannan

Gaza: Saudiyya Ta Kira Taron Musulmai, Fafaroma Ya Tsawata Wa Isra'ila

Malam Musa Abba Gana ya yi aikin N-Power daga shekarar 2018, ya shaidawa Legit cewa har aka yaye su, ba su bi gwamnati bashin kudi ba.

Sai dai malamin makarantar sakandaren ya bayyana cewa a lokacinsu, ba su samu na'urar da aka rabawa masu aikin naN-Power da farko ba.

Abba zai kai yara kasar waje

Idan aka shiga Kano, labari ya iso cewa Gwamnatin Kwankwasiyya ta kashe N1.3bn wajen biyawa mutum 57, 000 kudin NECO da na NBTE.

Sannan a makon nan za a fara aika yara karatu zuwa ketare bayan raba kyautar kayan makaranta, kuma za a gina karin makarantu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng