Shugaba Tinubu Na Shirin Gabatar da Naira Tiriliyan 26 a Matsayin Kasafin 2024
- Gwamnatin Bola Tinubu na shirin gabatar da jimullar Naira tiriliyan 26 a matsayin kasafin kuɗin shekarar 2024
- Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren ƙasa, Atiku Bagudu, ne ya bayyana haka ga 'yan jarida a Abuja bayan taron FEC ranar Litinin
- Bagudu ya ƙara da cewa za a miƙa kasafin kuɗin 2024 ga majalisar tarayya daga nan zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya karƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na shirin gabatar da kasafin kuɗi na 2024 wanda ya kai jimullar ƙudi N26tr.
Gwamnatin na shirye-shiryen miƙa kasafin ga majalisar tarayya kowane lokaci daga yanzu zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.
Ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Alhaji Atiku Bagudu, ne ya bayyana adadin kuɗin da kasafin 2024 ya ƙunsa bayan karƙare taron majalisar zartarwa (FEC) ranar Litinin.
Taron FEC karo na biyu karƙashin jagorancin shugaba Tinubu ya gudana ne yau 16 ga watan Oktoba, 2023 a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu zai ɗora daga inda Buhari ya tsaya wajen kasafin kuɗi
Kafin zuwan Tinubu, gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta ɗauki al'adar miƙa kasafin kuɗi ga majalisar tarayya kafin 31 ga watan Disamba, 2023.
Ga dukkan alamu Bola Tinubu na shirin ɗora wa daga nan yayin da Bagudu ya sanar cewa za a miƙa kasafin 2024 daga nan zuwa ƙarshen watan Disamban 2023.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, Gwamnatin tarayya ba ta yi bayani dalla-dalla kan abin da kasafin ya kunsa ba, ma'ana adadin kuɗin da aka ware wa kowane ɓangare.
A wurin taron FEC na yau Litinin wanda shugaba Tinubu ya jagoranta, an rantsar da ƙarin Ministoci uku da majalisar dattawa ta tantance su kwanakin baya, The Nation ta ruwaito.
Murna Yayin Da Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Ranar Biyan Basusukan Masu N-Power
A wani rahoton kuma Gwamnatin Tarayya ta ce a shirye ta ke ta fara biyan basusukan da wadanda ke shirin N-Power ke bin ta.
Masu kula da shirin na N-Power ne suka sanar da hakan yayin taro da wasu masu amfana da shirin a taron a Abuja.
Asali: Legit.ng