Jami’ar Aliko Dangote a Kano Ta Karyata Jita-Jitar Cewa Ta Na Daukar Aiki
- Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a jihar Kano ta yi karin haske kan labarin kanzon kurege da ake ta yadawa a kafafen sadarwa
- Jami’ar ta karyata jita-jitar cewa ta na daukar ma’aikata a makarantar inda ta ce labarin ba shi da tushe bare makama, ta gargadi mutane kan lamarin
- Mataimakin magatakardar Jami’ar, Mallam Abdullahi Datti shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Litinini 16 ga watan Oktoba a Kano
Jihar Kano – Hukumar gudanarwa ta jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote a jihar Kano ta karyata jita-jitar cewa ta na daukar aiki.
An yi ta yadawa a kafafen sadarwa cewa ADUSTECH ta fara daukar ma’aikata inda ta karyata hakan, Legit ta tattaro.
Meye Jami'ar ta ce kan daukar aiki a Kano?
Mataimakin magatakardar jami’ar, Malam Abdullahi Datti shi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a yau Litinin 16 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Hukumar wannan jami’ar ta na son fayyace cewa labarin cewa ta na daukar ma’aikata karya ne, saboda haka jama’a su yi watsi da ita.”
Daily Trust ta tattaro Datti na kira ga al’umma da su guji yada jita-jita wanda ya ke karkatar da hankalin jama’a.
Wasu tsare-tsare Jami'ar ta dauka a Kano?
A Jami’ar har ila yau, hukumomin makarantar sun amince da fara amfani da tsarin Babban Bankin Najeriya, CBN wurin biyan kudin makaranta ta e-Naira.
Shugaban Jamai’ar, Farfesa Musa Tukur Yakasai ya bai wa Bankin CBN tabbacin fara amfani da tsarin cikin kankanin lokaci bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar.
CBN ya fara wayar da kan mutane kan amfani da tsarin don saukaka al’amura a Najeriya.
Jami’ar Legas ta rage kudin makaranta bayan zanga-zangar dalibai
A wani labarin, hukumomin Jami’ar Legas sun ji ta dalibai inda su ka rage kudin makaranta da su ka kara a kwanakin baya.
Jami’o’in Najeriya da dama musamman na Gwamnatin Tarayya ne dai su ka kara kudaden makaranta na dalibai saboda tsadar rayuwa.
Wannan na zuwa ne bayan daliban Jami’ar sun yi ta yin zanga-zanga na kwanaki a harabar makarantar kan abin da su ka kira rashin tausayi.
Asali: Legit.ng