Lauya Falana Ya Ce Nadin Shugabannin EFCC da ICPC a Yanki Daya Ya Sabawa Doka
- Nadin sabon shugaban hukumar EFCC ya fara samun tasgaro yayin da lauyoyi ke ganin rashin dacewar nadin
- Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin shugaban EFCC wanda ya fito daga yankin Kudu maso Yamma
- Sannan shugaban hukumar ICPC, Bolaji Owasanoye shima ya fito yanki daya da shugaban EFCC wanda ya saba doka
FCT, Abuja – Shahararren lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Femi Falana ya ce nadin shugabannin hukumomin yaki da cin hanci na EFCC da ICPC a yanki daya ya sabawa doka.
Falana ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Litinin 16 ga watan Oktoba.
Meye Falana ya ce ga Tinubu kan EFCC, ICPC?
Ya bayyana cewa idan aka nada shugaban EFCC daga yankin Arewa ya kamata shugaban ICPC ya fito daga yankin Kudancin kasar, Legit ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan ya soki nadin Ola Olukoyede da Shugaba Tinubu ya yi a matsayin shugaban EFCC wanda ya fito daga yankin Kudu maso Yamma inda ya ce ya kamata a bi tsari wurin nadin mukamai.
Ya ce:
“Idan za a nada shugabannin EFCC da ICPC, ba za su fito daga yanki daya ba, idan akwai gurbin mukamai guda biyu, dole daya daga Kudu daya kuma daga Arewa.
“Idan kuma akwai gurbin guda hudu, dole biyu su kasance a Kudu biyu kuma su kasance a Arewacin kasar."
Wane shawara Falana ya bai wa Tinubu kan EFCC, ICPC?
Falana ya kara da cewa:
“Idan har kuma gurbin sun kasance guda shida, to dole ko wane yanki da ke kasar ya samu guda, wannan shi ne doka a Najeriya.”
Yayin da ya nuna gamsuwarshi da dacewa da mukamin, Falana ya nuna damuwarshi kan nadin dukkan shugabannin yaki da cin hanci a yankin Kudu maso Yamma, cewar Vanguard.
Tinubu ya nada Ola a matsayin shugaban hukumar EFCC
A wani labarin, shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci ta EFCC.
Ola ya kasance kwararren lauya wanda ya shafe shekaru a hukumar, zai yi wa’adin shekaru hudu bayan majalisa ta tantance shi.
Nadin na Ola na zuwa ne bayan dakatar da tsohon shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa daga mukaminsa.
Asali: Legit.ng