Budurwa Mayyar Boko Ta Kammala Digiri, Ta Gama da Makin da Ya Daga Hankalin Jama’a
- Budurwar da ta kammala digiri a kwanakin nan ta sha yabon jama'a bayan nuna kwazo a fannin karatunta
- Budurwar mai suna Deborah Danjuma Eleojo ta kammala digiri a fannin injiniyanci da maki mafi yawa; 5.0
- Deborah dai ta yi karatu ne a jami'ar Landmark, inda aka bayyana tarihin karatunta mai daukar hankalin gaske
Daga kammala karatun digiri budurwa mai suna Deborah Danjuma Eleojo ta shiga kafar sada zumunta zunzurutun yadda ta maida hankali ta yi karatu.
Dalibar da ta kammala digirinta a jami'ar Landmark da ke Omu-Aran a jihar Kwara tana da shaidar karatu tukuru.
Deborah dai ta kammala digiri da maki mafi girma; 5.0 kuma itace a fanninsu ta fi kowa samun maki mai yawa.
Labari ya bazu a kafar Twitter
Bayan kammala digirinta da kuma shagali da ahalinta, sai ta zo kafar Twitter don nunawa duniya abin da ta samu na arziki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta rubuta:
"Na gode ubangiji da kammala digiri na a fannin injiniyanci. 5.00/5.00."
Rubutun nata dai ya yadu ainun a kafar sada zumunta, inda mutane sama da dubu 376 suka gani tare da mutum kusan 12,000 ke dangwalen nuna sha'awarsu.
Martanin jama'a
Ga kadan kuma daga abin da mutane ke cewa:
@KennyNuga:
"5.00/5.00? Wannan ba zai taba faruwa ba a OAUIfe ko Unilag. Sai kin nuna kina da ilimi daidai da na Albert Einstein kafin ki samu wannan makin. Duk da haka, ina taya ki murna."
@_spirit_coder:
"Gaskiya, kinsan boko. Wani lokacin nakan tambaya a ina nake sadda ubangiji ke rabon baiwar ilimi. Ina matukar taya ki murna."
@Darlinnngton said:
"Samun 5.0/5.0 a injiniyanci ba karamin lamari bane. Ina taya ki murna."
Digirin Tinubu a kasar waje
A bangare guda, har yanzu ba a gama da batun shakku kan digirin Tinubu ba, an ba Atiku damar ya ga takardar da shugaban kasar ke boyewa.
Budurwa Da Ita Kadai Iyayenta Suka Haifa Ta Mutu Kwanaki 12 Bayan Ta Yi Bikin Kammala Jami’a a Facebook
Kotun Amurka ta ce, matukar dai an yi karatun nan, to babu batun a boye don haka a fito da digirin Tinubu Atiku ya gabatar a gaban kotu.
Ya zuwa yanzu, an yi shari'a a Amurka, an ce jami'ar Chicago ta tabbatar da fitar takardar kowa ma gani kawai a huta
Asali: Legit.ng