Matakai 5 da Aka Dauka Kan Shirin N-Power da Ya Kamata Kowa Ya Sani

Matakai 5 da Aka Dauka Kan Shirin N-Power da Ya Kamata Kowa Ya Sani

  • Gwamnatin Tinubu ta dakatar da shirin N-Power don gudanar da bincike da kuma gano lam'a
  • N-Power shiri ne da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo a shekarar 2016 can baya
  • An kirkiri shirin ne don ba matasa tallafi da gogewar aiki tare da rage zaman banza a fadin kasar

FCT, Abuja - Shirin gwamnatin tarayya na N-Power ya sake fitar da jawabi game da makomar masu cin gajiyarsa.

Idan baku manta ba, ministar jin kai Betta Edu ta sanar da dakatar da shirin N-Power har sai an yi bincike.

A cewar Edu, an samu wasu matsalolin da ke da alaka da rashin gaskiya ne har ta kai ga aka dakatar da shirin na N-Power.

Halin da ake ciki kan N-Power
Shirin N-Power da abin da ke cikinsa a yanzu | Hoto: @npower_ng, @betta_edu
Asali: Twitter

A wani sakon da gudanarwar N-Power ta wallafa a shafin X, an ce za a yi bincike mai zurfi na kwakwaf don gano musababbin duk wasu matsaloli.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Karin Haske Kan Basukan Watanni 8 Na Matasan N-Power, Ya Yi Musu Alkawari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, binciken zai kai ga tunanin hanyar da za a kawo don biyan masu cin gajiyar cikin sauki.

Ga abubuwa 5 da N-Power ke kai a yanzu

  1. Akwai bukatar bincike mai zurfi da kuma bin kwakwaf na binciken kudi.
  2. Akwai bukatar samar da tsarin biyan wadanda suke bin gwamnati bashi ta yadda ya dace.
  3. Akwai bukatar kawo hanyar sanya ido kan masu cin gajiyar shirin a inda suke ba da gudunmawar aiki.
  4. Akwai bukatar sanya ido kan tsarin biya don biya a kan lokaci kuka daidai da tsari.
  5. Akwai bukatar sake fasalin shirin da kuma samun damar daukar karin 'yan Najeriya su ci gajiyar shirin.

Shin 'yan N-Power za su sami damar samun cikon kudin da suke bin gwamnati bashi a nan gaba kadan?

Za a dauki sabbin 'yan N-Power da yawa

Gwamnatin tarayya ta ce kashe shirin N-Power zai samar da aikin yi ga matasa miliyan biyar nan da shekaru biyar masu zuwa a kasar nan, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gambo Haruna: Bakanuwa Mai Marayu 6 Da Ke Sana’ar Tura Baro

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Manajan shirye-shirye na N-Power, Akindele Egbuwalo ya fitar.

Egbuwalo, wanda ya bukaci ‘yan Najeriya su fahimci dalilin kashe shirin da kuma sake fasalin da ake yi, ya ce gwamnatin tarayya na kokarin kawo tsari mai kyau a shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.