Yadda Matar Aure Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Siyawa Mijinta Kyaututtuka, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Yadda Matar Aure Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Siyawa Mijinta Kyaututtuka, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Bidiyon wata mata wacce ta kashe miliyoyi wajen siyawa mijinta kyaututtuka daban-daban ya yadu a dandalin TikTok
  • An rahoto cewa matar ta kashe kudi masu yawan gaske domin siyawa sahibinta kayayyaki iri-iri kama daga takalma, riguna da sauran kayan ado
  • Mutane da dama sun jinjina mata kan wannan alkhairi da ta yi wa mijin nata, wanda ya fada a jinsin da ba kasafai suke samu kyaututtuka daga daya jinsin ba

Wani bidiyo mai tsuma zuciya na wata mata da ta kashe miliyoyin kudi don siyawa mijinta kyaututtuka na bazata ya ja hankalin TikTok.

Bidiyon, wanda aka yada a TikTok, ya nuna matar wacce ke cike da farin ciki yayin da ta nunawa duniya kayayyaki iri-iri da ta siyawa mijinta, wanda sam baya sane da shirinta.

Mata ta siyawa mijinta kyauttutuka masu tarin yawa
Yadda Matar Aure Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Siyawa Mijinta Kyauttutuka, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: @brownsucre24
Asali: TikTok

Kyaututtukan sun hada da takalma, riguna, agogo, turaruka, da sauran kayan jin dadi wanda zai sa kowani namiji ya ji shi na daban ne.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Fusata Ta Juye Ruwa a Gadonsu Na Sunna Saboda Miji Ya Ki Siya Mata Gashin Kanti

Mutane da dama sun yaba ma matar a kan wannan karamci da tunani nata, cewa da wuya ka ga mace ta kashewa mijinta kudi wajen siya masa kyaututtuka, domin a kodayaushe maza ake jiran su kashewa abokan zamansu kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya samu dubban mutane da suka kalla tare da yi martani a TikTok, wanda hakan ya sa ya yadu a dandalin.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a kan bidiyon matar da ta siyawa mijinta kyaututtuka

Ridwan E ya yi martaniL

"A yayin da ka samu matar da ke mayar da irin abun da ka yi mata."

Bakedbylewa:

"Na rantse aikin asiri ne."

User5380285370818:

"Wayyo Allah."

Legit Hausa ta tuntubi wasu mata da don jin ko za su iya yin irin haka ga mazajensu don kara dangon soyayya.

Malama Hadiza ta ce:

Kara karanta wannan

“Ba Ki Da Hankali Ne?” Wani Mutum Ya Kurma Ihu Bayan Ya Kama Mai Aiki Tana Wanke Masa Kayan Wuta Da Sabulu

“Me zai hana idan har shima yana yi mun. Duk matar da za ki ga ta yi wa mijinta irin haka ta san me take samu daga wajensa. Wallahi idan ana zaman dadi duk wannan abu mai sauki ne. Ko a yanzu ma a karamin karfina ina kamantawa tunda idan naga abun da na san yi masa kyau, ko na amfanin yara ina siya, kin ga kuwa ina kokari da shi.”

A nata bangaren Maman Nurain cewa ta yi:

“Zan iya kashewa Baban Nurain fiye da haka idan ina da shi, don shima ba baya ba wajen kyautata mun da yara. Menene amfanin zaman tare idan har ba za a kyautatawa juna ba? Allah dai ya kawo mana abun yi za a san muma ba daga baya ba.”

Yadda wata mata ta fado daga kan achaba, ta jike jagab da ruwan chabi a bidiyo

A wani labari na daban, wani bidiyo da ke nuna lokacin da wata mata ta fado daga babur sannan ta jike sharkaf da ruwan chabi a hanyar.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Gidan Magajiya Suka Bazama Neman Kwastamomi a Kasuwar Legas

A cikin bidiyon da @jab0010 ya wallafa, alamu sun nuna matar na hanyarta ta zuwa wani muhimmin wuri ne lokacin da lamarin ya afku.

Bidiyon ya nuna yadda dan achaban ya shiga wata hanya da ke cike da ruwa sannan ya yi kokarin kutsa kai ta ko halin 'ka'ka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng