Manya-Manyan Malaman Musulunci 5 da Su Ka Halarci Walimar Auren Gata a Kano
- Gwamnatin Kano ta aurar da mutane 1, 800 kuma ta gayyaci shehun malamai zuwa bikin auren da aka yi a gidan gwamnati
- An kira malamai daga bangarori da kungiyoyi dabam-dabam, wasu sun halarta yayin da wasu su ka aiko da wakilcinsu a taron
- Jagororin JIBWIS irinsu Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir da Muhammad Kabir Gombe sun halarci walimar da aka shirya
Kano - A ranar Juma’a, 13 ga watan Oktoba 2023, gwamnatin jihar Kano ta gudanar da auren gata a karkashin hukumar HISBAH.
Malaman addini sun halarci bikin da aka shiryawa ma’auratan bayan an daure auren a jiya.
An yi walimar ne a wata farfajiya da ke cikin gidan gwamnatin jihar Kano domin taya wadanda su ka yi auren murna da farin ciki.
A rahoton nan, mun kawo jerin sunayen malamai da su ka halarci walimar, a ciki har da Bishof Isaac Idahosa wanda jigo ne a NNPP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idahosa wanda shi ne abokin Rabiu Musa Kwankwaso a karkashin jam’iyyar NNPP a zaben shugaban kasa na 2023, babban fasto ne.
1. Aminu Ibrahim Daurawa
A matsyinsa na shugaban hukumar HISBAH, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sake jagorantar auren gatan da aka shirya a jiya.
2. Sani Yahaya Jingir
Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya halarci walimar, har ya gabatar da jawabi. A zaben 2023, ya bada shawarar a zabi NNPP a Kano.
3. Muhammad Kabir Gombe
Sakataren kungiyar JIBWIS na kasa, Muhammad Kabir Haruna Gombe ya je wajen walimar, ya kuma samu wuri a sahun gaba-gaba.
4. Aliyu Rasheed Makarfi
Ustaz Aliyu Rasheed Makarfi ya na cikin wadanda su ka tofawa taron albarka. Malamin ya yi suna wajen yin wa’azi a kan rayuwa da mu’amala.
5. Sani Shariff Bichi
Sheikh Sani Shariff Bichi wani shahararren malami ne da Legit ta hanga a wajen, shi ne shugaban majalisar malaman Kano na reshen Izalar-Jos.
Shawarar Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga ma'uratan da su guji leka wayoyin juna domin hakan shi ne babban abin da ya ke raba aure a zamanin nan.
An rahoto Kwankwaso ya na yabawa yadda Abba Kabir Yusuf ya farfado da manufofin gwamnatin Kwankwasiyya da ya kirkiro a Kano.
Asali: Legit.ng