Gwamna Sule Ya Ce Ba a Biya Kudin Fansa Ba Kafin Sako Daliban Jami'ar NSUK
- Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya yi tsokaci kan batun ceto ɗaliban jami'ar jihar Nasarawa da ƴan bindiga suka sace
- Gwamnan ya bayyana cewa ba a biya ko sisi a matsayin kuɗin fansa ba kafin a sako ɗaliban jami'ar
- A cewar gwamnan ƙoƙarin jami'an tsaro ne ya sanya aka ceto ɗaliban, inda ya jinjina musu kan namijin ƙoƙarin da suka yi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa ba a biya kuɗin fansa ba ga wadanda suka sace ɗalibai mata huɗu na jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) kafin a kuɓutar da su.
Gwamna Sule ya bayyana haka ne bayan ya kai ziyarar godiya ga kwamandan runduna ta 177 Guard Battalion, da ke Keffi, cewar rahoton Daily Trust.
Jaridar Vanguard ta ce an yi garkuwa da ɗaliban huɗu ne a gidansu da ke unguwar Agwan Kare a Keffi da sanyin safiyar ranar Talata, 10 ga watan Oktoban 2023.
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sake Sace Dalibai a Jami'ar Gwamnatin Tarayya Da Ke Gusau, Bayanai Sun Fito
Sai dai, bayan farautar da ƴan sanda da sojoji da sauran jami'an tsaro suka ƙaddamar, an kuɓutar da ɗaliban a ranar Alhamis da yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bayyana cewa an ceto ɗaliban ne a dazuzzukan da ke Agwan Gauta da ke Keffi, biyo bayan ƙoƙarin da jami'an tsaro suka yi.
Ko nawa aka biya a matsayin kuɗin fansa?
A cewar gwamnan, hukumomin NSUK da sojoji ba su biya kuɗin fansa ba kafin a ceto ɗaliban da aka sace.
A kalamansa:
"Ba ni da masaniya kan wasu kuɗin fansa. Da zarar jami'an tsaro sun matsa lamba kan masu garkuwa da mutane, ba na tunanin akwai batun kuɗin fansa."
"A iyakar sani na babu wani kuɗin fansa da aka biya. Jami'ar ba ta biya kuɗin fansa ba, haka ma sojoji ba su biya ba."
Gwamna Sule ya yaba wa jami'an tsaro
Gwamna Sule ya kuma shaida wa manema labarai cewa ya je barikin ne da kan sa domin miƙa godiyar shugaban ƙasa Bola Tinubu ga kwamandan bisa kokarin da suka yi na ceto ɗaliban.
Ya kuma nuna jin daɗinsa ganin yadda ɗaliban ke cikin ƙoshin lafiya, inda iyayensu suka yi shirin karɓar ƴaƴansu.
An Sake Sace Dalibai a FUGUS
A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun sake kai farmaki a jami'ar gwamnatin tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke Zamfara.
A yayin sabon farmakin da ƴan bindigan suka kai, sun yi awon gaba da ɗaliban jami'ar guda biyu, mace ɗaya da namiji ɗaya.
Asali: Legit.ng