MURIC Ta Soki Fasto Adeboye Kan Goyon Bayan Isra’ila a Yakin da Su Ke da Falasdinu
- Kugiyar Kare Hakkin Musulmai, MURIC ta caccaki Fasto Adeboye kan nuna goyon bayan Isra’ila da ya yi a makon da ya gabata
- Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya shawarci Adeboye da ya yi addu’ar samun lafiya a duniya madadin hakan
- A makon da ya gabata ne Fasto Adeboye ya fito karara tare da nuna goyon baya da kuma addu’a ga kasar Isra’ila
FCT, Abuja - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta soki Fasto Enoch Adeboye kan nuna tsaginshi a fadan da ake tsakanin Isra’ila da Falasdinu.
Kungiyar ta shawarci Adeboye da ya yi addu’a ga samun zaman lafiya a duniya ba wai goyon bayan Isra’ila ba, Legit ta tattaro.
Meye MURIC ta ce ga Adeboye kan Isra’ila/Falasdinu?
Daraktan hukumar, Farfesa Ishaq Akintola shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Asabar 14 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akintola ya bukaci Adeboye da ya yi addu’ar tarwatsewar masu hannu a cikin rikicin da ke faruwa tsakanin Isra’ila da Falasdinu.
A makon da ya gabata ne Legit Hausa ta ruwaito cewa Fasto Adeboye ya nuna goyon bayanshi da yin addu’a ga kasar Isra’ila a cikin wani faifan bidiyo da ya fitar, cewar Vanguard.
Wane sako MURIC ta tura wa Adeboye kan Isra’ila/Falasdinu?
Sanarwar ta ce:
“Mun samu labarin cewa shugaban cocin RCCG, Enoch Adeboye ya nuna goyon bayanshi ga kasar Isra’ila yayin da ake ci gaba da gwabza ya ki tsakaninsu da Falasdinu.”
“Mun kadu da jin wannan matsaya ta Adeboye wanda bai duba wahalar da mutane ke sha ba tare da cin zarafinsu a ko wace rana ba tare da kasashe sun dauki mataki ba,”
Farfesan ya ce rikicin da ke tsakanin kasashen biyu ba addini ba ne ya jawo illa matsalar rikicin iyakoki.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su bari rikicin ya rarraba musu kawuna madadin haka su yi addu’ar samun zaman lafiya da kaunar juna.
Fasto Adeboye ya nuna goyon baya ga Isra’ila
A wani labarin, shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya bayyana goyon bayanshi ga kasar Isra’ia yayin da su ke ci gaba da gwabza yaki da Falasdinu.
Adeboye ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo inda ya ke musu addu’ar samun nasara.
Asali: Legit.ng