Rundunar ’Yan Sanda a Borno Ta Dakile Yunkurin Sace Taragon Jirgin Kasa

Rundunar ’Yan Sanda a Borno Ta Dakile Yunkurin Sace Taragon Jirgin Kasa

  • Jami’an ‘yan sanda a jihar Borno sun cafke wasu da ake zargi da yunkurin sace taragon jirgin kasa
  • Rundunar ta ce ta yi nasarar cafke wadanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri daga jama’a
  • Ta ce lamarin ya faru ne a yau Asabar 14 ga watan Oktoba a tashar jirgin kasan da ke birnin Maiduguri a jihar

Jihar Borno – Rundunar ‘yan sanda a jihar Borno ta dakile shirin sace taragon jirgin kasa a tashan jirgin da ke Maiduguri a jihar.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 14 ga watan Oktoba inda su ka ce ‘yan sanda sun cafke wadanda ake zargin har mutane 6, Legit ta tattaro.

'Yan sanda sun cafke wasu da zargin satar taragon jirgin kasa a Borno
Yan Sanda Sun Kama Wasu Kan Yunkurin Sace Taragon Jirgin Kasa. Hoto: @ZagazOlaMakama.
Asali: Twitter

Meye ake aka sata a jirgin kasa a Borno?

Jami'an ‘yan sanda sun tabbatar da nasarar cafke wasu daga cikinsu ne bayan samun bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Ana Cikin Yanayi Bayan ’Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Bas a Jihar Arewa, Mutum 1 Ya Mutu, An Raunata 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta tattaro cewa lamarin ya faru kamar haka:

“An dakile shirin satar taragon jirgin kasa a Maiduguri bayan samun bayanan sirii daga wasu mutanen kirki.
“Wadanda ake zargin tuni su ka shiga hannun jami’an sanda tare da tafiya da su don bincike.”

Kakakin Hukumar Jiragen Kasa, NRC, Mahmood Yakubu ya ce ba shi da labarin faruwar lamarin inda ya ce sai dai a tuntubi manajan hukumar na yankin Arewa.

Har ila yau, kokarin jin ta bakin manajan yanki na hukumar NRC ya ci tura inda wayarsa ta kasance a rufe.

Wane martani 'yan sanda su ka yi kan satar a Borno?

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Sami Kamilu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mutane shida sun shiga hannun jami'ansu.

Kamilu ya ce:

"Tabbas, haka ne, ba za mu iya kiyaye yawan taragogin ba har yanzu amma da gaske ne hakan ta faru.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mahaifyar Sanata Ahmed Lawan Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

"Mun yi nasarar kama wadanda ake zargi har mutane shida, wannan shi ne iya abin da zan iya fama muku."

'Yan sanda sun kama matar da ta watsa wa mijinta man gyada mai zafi

A wani labarin, 'Yan sanda a jihar Ribas sun cafke matar da ta watsawa mijinta tafasasshen man gyada a jihar.

Matar mai suna Hope Nwala ta aikata hakan ne bayan 'yar wata hatsaniya a tsakaninta da mijinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.