Gambo Haruna: Matar Da Ke Tura Baro Domin Ciyar Da Marayunta 6 a Kano

Gambo Haruna: Matar Da Ke Tura Baro Domin Ciyar Da Marayunta 6 a Kano

  • Gambo Haruna, wata bazawara wacce mijinta ya mutu shekaru shida da suka wuce, tana fadi tashi don kula da yaransu guda shida
  • Rahotanni sun tabbatar da cewar matar na siyar da ruwa a baro domin kula da rayuwar yaranta
  • Ta ce tana samun kamar N750 zuwa N1,000 a kullun, wanda baya isarta siyan koda sinkin babban biredi guda daya

Ungogo, Kano - Rahotanni sun tabbatar da cewar wata mata mai matsakaicin shekaru wacce mijinta ya mutu shekaru shida sakamakon rashin lafiya, Gambo Haruna, tana fama da matsin rayuwa.

An rahoto cewa ta shafe tsawon shekaru biyu tana sana'ar tura ruwa a baro domin kula da yaranta guda shida.

Mijin Gambo ya rasu ya bar ta da marayu shida
Gambo Haruna: Matar Da Ke Tura Baro Domin Ciyar Da Marayunta 6 a Kano Hoto: @aljazirahnig
Asali: Twitter

Tana rayuwa ne a cikin wani gidan laka a Gadar Katako, da ke yankin Rimin Kebe na karamar hukumar Ungogo da ke jihar Kano, wanda take biyan kudin haya N12,000 duk shekara.

Kara karanta wannan

“Babu Likita”: Mahaukaciya Ta Haifi Kyakkyawan Jinjiri Fari Shar Da Shi, Hotunan Sun Yadu

Wannan kalubale na rayuwa da take fuskanta ya sa ta tsufa da kuruciyarta, amma duk da haka tana fadi tashi don ganin ta shawo kansu ba tare da ta fada harkar bara ko abubuwan da bai dace ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gambo na kallon wannan hali da take ciki a matsayin nufin Allah sannan ta ce tana fatan samun haske a rayuwarta na gaba.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, ta ce:

"Wahala ce ta sa na fara tura baro don siyar da ruwa da kuma ciyar da iyalina. Ban san me zan iya yi ba kuma. Na shafe tsawon shekaru biyu a matsayin mai ruwa."

Ta yi bayanin halin da take ciki, cewa tana aiki ba ji ba gani a matsayin mai ruwa don ciyar da iyalinta.

Ta ce a baya ta yi aiki a matsayin lebura a wani kamfani sannan ta dogara da abincin sadaka. Ta ce ta jajirce wajen tura yaranta makaranta, don tana ganin ilimi shine tikitin samun rayuwa mai inganci.

Kara karanta wannan

Ta Shafe Shekaru 20 Tana Tara Kudi: Yadda Shagalin Bikin Wadda Ta Auri Kanta Da Kanta Ya Gudana

Ta ce:

"Ba na so yarana su taso ba tare da ilimi ba; wannan ne dalilin da yasa nake yin wannan. na san cewa da wannan kawai, da na cimma manufata a rayuwa sannan rayuwarsu ba za ta zamo kamar nawa ba."

Duk da wahalar da ke tattare da sana'arta na ruwa, Gambo tana samu akalla N750 zuwa N1,000 a kullun, wanda daga ciki tana biyan N150 kudin aron baro. Ba ita ke da baron ba amma tana haya don ta kula da iyalinta.

Gambo ta tuna yadda mijinta ya mutu

Koda dai tana fuskantar kalubale daban-daban kuma tana ganin an wareta a al'ummarta, daya daga cikin malaman yaranta ya sauke mata nauyin kudin makarantarsa, kuma karamcin da suke samu daga sauran mutane yana taimaka masu.

Gambo tana neman karin tallafi domin kawo sauki ga gwagwarmayarsu da kuma daukar nauyin yaranta.

An tattaro cewa yanayin rayuwarsu ba shi da sauki, kuma suna biyan hayar N1,000 duk wata ko N12,000 duk shekara.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Fusata Ta Juye Ruwa a Gadonsu Na Sunna Saboda Miji Ya Ki Siya Mata Gashin Kanti

Mijinta ya yi aiki a matsayin karamin ma’aikaci da gwamnatin jihar amma ya rasa aikinsa a gwamnatin da ta gabata.

Daga baya ya yi sana’ar tuka babur kafin gwamnati ta haramta irin wadannan ayyuka, kuma a karshe ya rasu sakamakon karancin jini.

“Ya koma aikinsa na share gefen titi, daga baya ya zama dan achaba kafin gwamnati ta hana shi. Zan iya tunawa ko a lokacin rayuwar babu dadi sosai, daga baya ya mutu sakamakon karancin jini.”

Mai lalurar tabin hankali ta haifi kyakkyawan yaro

A wani labarin, mun ji cewa wata mata mai lalurar tabin hankali ta haifi kyakkyawan jinjiri, kuma hotunan sun yadu.

Gabby Queens ce ta wallafa hotunan matar da danta a Facebook, kuma sun tsuma zukatan mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng