Daga Daki Daya Zuwa Gida Mai Kyau: Ma’auratan Da Ke Tare Tun Suna Talakawa Sun Kudance, Bidiyonsu Ya Yadu

Daga Daki Daya Zuwa Gida Mai Kyau: Ma’auratan Da Ke Tare Tun Suna Talakawa Sun Kudance, Bidiyonsu Ya Yadu

  • Mabiya shafukan soshiyal midiya sun jinjinawa soyayyar wasu ma’aurata kan yadda suka kasance da junansu tun basu da komai har Allah ya azurta su
  • Ma’auratan sun fara rayuwarsu a lokacin da suke cikin kangin rayuwa kuma a cikin fallen daki daya da babu komai a ciki
  • Shekaru bayan nan, harkoki sun budewa miji da matan kamar yadda ya bayyana a hotunan sabuwar rayuwarsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wasu ma’aurata sun burge jama’a a soshiyal midiya kan yadda suka kasance tare da junansu cikin ritsi cikin wuya.

Wani bidiyo da ke nuna yadda suka sha gwagwarmayar rayuwa ya bayyana a shafukan soshiyal midiya kuma tuni ya yadu.

Ma'aurata
Daga Daki Daya Zuwa Gida Mai Kyau: Ma’auratan Da Ke Tare Tun Suna Talakawa Sun Kudance, Bidiyonsu Ya Yadu Hoto: TikTok/@akaemmanuel8
Asali: UGC

Bidiyon da aka yada a TikTok ya nuna yadda ma’auratan suka fara rayuwar aurensu a cikin daki falle daya.

Hotunan dakin wanda yake a hargitsa babu kayan azo a gani ya nuna yadda suka tattara komai nasu a waje guda, ciki harda wata babur.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 3 Da Aure Ba Tare Da Sun Ga Juna Ba, Yar Najeriya Ta Hadu Da Baturen Mijinta A Amurka

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da haka sun yi hakuri sannan suna baccinsu tare. Kamar yadda yake a hoton, matar kan kwanta a kan kujera inda shi kuma mijin ke kwanciya a wani dan yololon katifa a kasa.

Sabbin hotuna sun nuna ma’auratan wadanda yanzu suka samu yalwa kuma sun kara haske sannan sun mallaki sabon gida.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

tochiuju ta ce:

"Maza kada ku manta da wadanda suka tsaya da ku a lokacin da kuke cikin talauci."

mercy ta ce:

"Jinjina ta musamman ga wannan mutumin. yawancin maza da ke tsintar kansu a wannan halin sun gwammaci jin dadi da macen da bata sha wuya da su ba."

user4458758732770 ya ce:

"Samun irin matan na da wuya a yanzu Allah ya albarkace ta."

Misidollar ta ce:

Kara karanta wannan

Ya Guje Mu Saboda Baya Son Tagwaye: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Da Yan Biyunta Ya Ba Da Mamaki

"Allah ya albarkaci aurenki yar'uwa amma ni ba zan sake shan wuya da namiji ba ni na san me idanuna suka gani."

Bayan Shekaru 3 Da Aure Ba Tare Da Sun Ga Juna Ba, Yar Najeriya Ta Hadu Da Baturen Mijinta A Amurka

A wani labarin, wata matashiya da ke soyayya da wani bature ta samu damar haduwa da shi shekaru uku bayan aurensu.

Kafin tafiyarta, matar ta yi cikakken bidiyo don nuna irin shirin da tayi kama daga gyaran jiki har zuwa na gashi.

Ana gobe za ta koma Amurka, matar ta gyara gashinta tayi kitso yayin da take rera wakar Naira Marley na zuwansa Amurka na farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel