Agbakoba Ya Bayyana Dabarar da FG Za Ta Yi Farashin Man Fetur Ya Dawo N300

Agbakoba Ya Bayyana Dabarar da FG Za Ta Yi Farashin Man Fetur Ya Dawo N300

  • Olisa Agbakoba ya bayyana cewa za a iya samun raguwar farashin man fetur zuwa Naira 300 kan kowace lita
  • Babban lauyan ya ba da dabarar da FG za ta bi domin cimma wannan ƙudirin na rage farashin man fetur
  • Ya ba da shawarar cewa ya kamata NNPC ya rika samar da danyen mai ga matatun mai a Najeriya a farashin naira maimakon dala

Olisa Agbakoba, tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), ya shawarci gwamnatin tarayya kan yadda za a rage farashin man fetur zuwa Naira 300 kan kowace lita.

Agbakoba, babban lauyan Najeriya (SAN), ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) da su yi la'akari da wasu dabaru na ganin an rage farashin man fetur.

Olisa Agbakoba ya shawarci FG
Agbakoba ya bayyana yadda FG za ta rage farashin man fetur Hoto: Ardova Plc, Olisa Agbakoba Legal
Asali: UGC

Tun bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Mayun 2023, farashin man fetur ya tashi sama kusan aƙalla sau biyu.

Kara karanta wannan

Bayan Ganin Kamun Ludayin Tinubu, Kiristocin Najeriya Sun Canza Tunani Kan Tikitim Musulmi da Musulmi

A halin yanzu ana siyar da man fetur tsakanin N580 zuwa N617, ya danganta da yankin da wurin da mutum yake a ƙasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan dai na faruwa ne yayin da ƴan kasuwar man suka yi barazanar cewa farashin man zai iya ƙaruwa zuwa Naira 800 kan kowace lita a makonni masu zuwa, ganin yadda aka samu ƙarin kudin daƙon man fetur ɗin.

Sayar da danyen mai ga matatun mai a naira

A cewar Agbakoba, ba tsari ba ne cewa NNPCL na sayar da danyen mai ga matatun man Najeriya da dala.

Yayin wata tattaunawa da jaridar Vanguard, fitaccen lauyan ya bayar da shawarar cewa ya kamata NNPC ta samar da ɗanyen man fetur ga matatun mai da dama a fadin ƙasar nan akan kayyadadden farashin naira maimakon dala.

A kalamansa:

"Farashin zai sauka zuwa N300. Ina ƙalubalantar NNPC ya gwada hakan, farashin zai sauka. Amma idan ka sayar da shi a kan farashin kasuwannin duniya, ta yaya masu sayar da shi a cikin gida za su samu dala su siya sannan daga baya su sayar da Naira? Dole ne su ɗaga farashin! Wannan ita ce matsalar."

Kara karanta wannan

Ombugadu Na PDP Ya Yi Martani Kan Batun Cewa Zai Tube Rawanin Sarakuna Da Zarar Ya Hau Mulki a Nasarawa

Majalisa Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Sabuwar Hukuma

A wani labarin kuma, majalisar wakilai ta samo hanyar da za a magance hawan tashin farashin kayayyaki a ƙasar nan.

Majalisar ta buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya kafa hukumar da za ta riƙa kula da ƙayyade farashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng