“Ya Yi Nasara a Kararraki 26": Lauyan Bogi Ya Je Kotu Don Kare Mutane, Ya Yi Nasara a Shari’o’i

“Ya Yi Nasara a Kararraki 26": Lauyan Bogi Ya Je Kotu Don Kare Mutane, Ya Yi Nasara a Shari’o’i

  • Wani mutum da ake zargin lauyan bogi ne ya kare wasu mutane a gaban kotu kuma ya yi nasarar lashe kararraki da dama
  • Mutumin mai suna Brian Mwenda Njagi ya tsayawa mutane a kararraki 26, kuma gaba daya shine a sama
  • Asirin Brian ya tonu ne bayan kungiyar lauyoyi a yankin ta gano cewa yana yiwa wani lauya sojan gona ne

Wani mutumi wanda ake zargin lauyan bogi ne ya yi nasarar lashe kararraki 26 a kotu kafin aka gano shi.

An yi zargin cewa mutumin, Brian Mwenda Njagi, yana yi wa wani lauya mai irin sunansa sojan gona ne.

An kama wani Lauyan bogi
“Ya Yi Nasara a Kararraki 26: Lauyan Bogi Ya Je Kotu Don Kare Mutane, Ya Yi Nasara a Shari’o’i Hoto: Citizen Digital
Asali: UGC

Kamar yadda kungiyar lauyoyin na Kenya ta bayyana, ainahin lauyan da ake yi wa sojan gona sunansa Brian Mwenda Ntwiga.

Lauyan bogi ya wakilci mutane a kotu kuma ya yi nasara a kararraki

Kara karanta wannan

Abin Takaici Yayin da Lauyoyi Su Ka Doku da Jifa da Kujeru a Cikin Kotu, Bidiyon Ya Jawo Cece-kuce

Ainahin lauyan, Brian Mwenda Ntwiga, ya samu shiga kungiyar amma ba a riga an ba shi satifiket dinsa na fara aiki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto cewa shi lauyan na bogi, Brian Mwenda Njagi, ya samu yin kutse a shafin yanar gizon kungiyar sannan ya nemi satifiket din fara aiki da bayanan ainahin lauyan.

Citizen Digital ta nakalto kungiyar lauyoyin na cewa:

"A ranar 5 ga watan Agustan 2022, Brian Mwenda Ntwiga ya samu shiga kungiyar lauyoyi kuma an dauki bayanan ainahin shafinsa na imel sannan aka bude masa shafi a shafin yanar gizon kungiyar.
"Mun tuntubi Brian Mwenda Ntwiga, wanda ya tabbatar da cewar bai nemi a yi masa satifiket din fara aiki ba tun bayan shigarsa kungiyar, dalili kuwa shine cewa yana aiki a ofishin Atoni Janar kuma baya bukatar satifiket din fara aiki.

Kara karanta wannan

Gowon, Akeredolu Da Wasu Fitattun Yan Najeriya 4 Da Aka Yi Karyan Sun Mutu

"Har sai da wani lokaci a Satumban 2023 lokacin da ya yi yunkurin shiga shafin da kuma farfado da bayanansa da nufin neman satifiket din fara aiki, a lokacin ne ya gane cewa ya gasa shiga shafin nasa."

Brian Mwenda Njagi ya yi wa wani lauya sojan gona

Da fara bincike sai aka gano cewa shi lauyan bogin, Brian Mwenda Njagi ya sauya hoton ainahin lauyan sannan ya sanya nasa a shafin yanar gizon kungiyar.

Kungiyar lauyoyin ta yi kira ga kama Brian Mwenda Njagi. Labarin ya yadu, kuma Naira PR ta wallafa shi a dandalin X, kuma ya samu martani da dama.

Kalli labarin a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Iselema ya ce:

"Ku tura shi makarantar lauyoyi, kwararren lauya ne mara digiri."

@godsentkalu123 ta ce:

"Kawai a mallaka masa shaidar digiri a bangaren karatun lauya."

@Oluchima1 ta ce:

"Irin wadannan mutane ba a hukunta su. Maimakon haka a taimaka masa ya zama tauraron da yake son zama."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Gidan Magajiya Suka Bazama Neman Kwastamomi a Kasuwar Legas

An Kwamushe Alkali Ya Na Rubutawa Budurwarsa Jarrabawa, An Tasa Keyarsa Zuwa Gidan Kaso

A wani labari na daban, mun ji cewa an garkame wani alkali bayan samunsa da laifin rubutawa budurwarsa jarrabawa a kasar Uganda.

Wanda ake zargin Semwogerere Ammaari Musa, an kama shi ne a Cibiyar Lauyoyi (LCD) a Uganda, Legit.ng ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng