Kwankwaso da Abba Kabir Sun Ɗaura Auren Ma'aurata 1,700 a Jihar Kano
- 'Yan uwa da abokan arziƙi ne suka halarci babban Masallacin Kano domin shaida auren zawarawa da yan mata 1,800
- Kwankwaso ne wakilin Anguna yayin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya kasance waliyyin amare kuma gwamnatin Kano ta ɗauki nauyi
- Babban limamin Kano ne ya jagoranci ɗaura auren wanda aka biya sadakin N50,000 ga kowace Amarya a madadin Anguna
Jihar Kano - Jagoran ɗariƙar Kwanwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso, da gwamna Abba Kabir Yusuf, sun ɗaura auren 'yan mata da zawarawa 1,800 yau Jumu'a.
Wannan gagarumin biki da aka raɗa wa Auren Gata, ya haɗa ma'aurata ango da amarya kimanin 1,800 kuma gwamnatin Jihar Kano ta ɗauki nauyin komai da komai.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an ɗaura waɗan nan aurarraki a babban Masallacin fadar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Kwankwaso ne ya zama wakilin dukkan Angwaye yayin da Gwamna Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ne waliyyin amare 1,800 da aka ɗaure su yau Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka raba auren zawarawa a wannan karon
Duk da an saba ɗaura auren a wuri ɗaya amma a wannan karon ma'aurata 330 aka ɗaura wa aurensu a karamar hukumar Birni da Kewaye.
Sauran kuma an ɗaura su a matakan kananan hukumomi domin ta haka ne kaɗai za a rage cunkoson jama'a da kuma zirga-zirga.
Babban Limamin Kano, Farfesa Sani Zahraddeen, shi ne ya jagoranci haɗa wannan Sunnah kuma an mika sadakin Naira 50,000 a madadin kowane ango ga amarya.
Idan baku manta ba, Rundunar yan sandan Musulunci watau Hisbah ta jihar Kano ta ce aƙalla ma'aurata 4,000 suka yi rijistar neman a haɗa su aure.
Hisbah ƙarƙashin jagoran Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ta ce ta zaɓi ma'aurata 1,800 daga cikin waɗan da suka nuna sha'awar shiga shirin auren gata.
Bayan haka hukumar Hisbah ta shirya yi musu gwajin lafiya domin tabbatar da afiyarsu gabanin a haɗa su aure.
Gwamnatin Kano Ta Aike da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Sanata Bello Yusuf
A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi ta'aziyyar rasuwar Sanata Bello Maitama Yusuf (Sardaunan Dutse).
Gwamnan ya ayyana mutuwar Sanata Bello a matsayin babban rashi ba wai ga iyalansa kaɗai ba, har da ƙasa baki ɗaya.
Asali: Legit.ng