“Kuna Da Sauran Mako 3 Don Biyan N4.5m”, NAHCON Ga Maniyyata Aikin Hajji
- Hukumar kula da Alhazai a kasar nan ta ba maniyyata mako uku don su biya kudin kujerar hajjin 2024
- NAHCON ta bukaci masu niyan zuwa hajjin badi da su biya naira miliyan 4.5 cikin mako uku masu zuwa
- Hukumar aikin hajjin ta ce Saudiyya ta tsayar da ranar 4 ga watan Nuwamba da don kammala tsare-tsare da dukkan masu ruwa da tsaki
Hukumar da ke kula da Alhazai a Najeriya (NAHCON), ta ce saura mata mako uku don tattauna farashin kujera a kasar Saudiyya, saboda haka ta bukaci maniyyata da su biya naira miliyan 4.5 kafin lokacin.
Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, cewa Saudiyya ta ajiye ranar 4 ga watan Nuwamba, don kammala shirye-shirye da masu ruwa da tsaki.
Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Dalilin da Ya Sa Ba Za Ta Iya Dakile Matsalar Aikin Yi Ba a Najeriya, Ta Tura Roko
Saudiyya ta ba da 4 ga watan Nuwamba domin kammala shirye-shiryen hajjin 2024
Ta bayyana cewa a lokacin ne NAHCON za ta kiyasta yawan maniyyata domin tattauna farashin kujera tare da yanke shi, jaridar Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanda ta kuma bayyana cewa shirye-shiryen da suka fara da wuri ne ya sa hukumar da shugabannin Hukumomin Alhazai na jihohi suka sanar da naira miliyan 4.5 a matsayin kudin kujerar aikin hajjin 2024.
Sanarwar ta ce:
"Hikimar da ke tattare da fara ajiye wannan kudade ya ta'allaka ne a kan dalilai uku. Na farko ya kasance saboda jihohi da hukumar su san yawan alhazan da za a lissafa a matsayin maniyyata hajji nan da ranar 4 ga watan Nuwambar 2023, wanda shine lokacin da Saudiyya ta tsayar don kammala shirye-shirye da masu ruwa da tsaki.
"Sanin adadin maniyyatan zai taimaka wa hukumomin wajen yin duk tsare-tsaren da suka dace a kan lokaci."
Ta kara da cewar an tsayar da wannan farashi ne domin ba maniyyata daman cika ragowar kudaden sannu a hankali zuwa lokacin da za a sanar da ainahin farashin kujerar.
Kakakin hukumar ta kuma ce duk wadanda suka gaza biyan adadin da aka fara kayyadewa, to su kuka da kansu idan aka kirga yawan maniyyatan 2024 babu sunansu ciki, rahoton Aminiya.
Yadda alhazan Kano 9 suka barke da gudawa a Makkah bayan kammala aikin Hajji, an bayyana dalili
A wani labarin, hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da barkewar gudawa a sansanin mahajjatan jihar Kano a Makkah.
Jami'an kiwon lafiya na hukumar su suka tabbatar da haka ta bakin shugabansu, Dakta Usman Galadima a ranar Lahadi 9 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng