Tinubu Ya Saba Doka Wajen Nadin Sabon Shugaban EFCC Inji Tsohon Jigon APC

Tinubu Ya Saba Doka Wajen Nadin Sabon Shugaban EFCC Inji Tsohon Jigon APC

  • Daniel Bwala ya zargi Bola Ahmed Tinubu da sabawa dokar kasa wajen nada sabon shugaban da zai jagoranci EFCC
  • A matsayin na lauya, tsohon ‘dan jam’iyyar ta APC ya kafa hujja da doka, ya ce Olu Olukayode bai cancanta da kujerar ba
  • Mista Olu Olukayode ba jami’in tsaro ba ne, kuma wasu su na ikirarin bai kai shekaru 15 ya na aikin lauya a Najeriya ba

Abuja - Nadin Olu Olukayode da Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin shugaban hukumar EFCC a Najeriya ya jawo abin magana.

Daniel Bwala wanda ya ke da ilmin shari’a kuma masanin dokoki, ya yi tsokaci a game da nadin a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

A ra’ayin Daniel Bwala, nadin Olu Olukayode ya ci karo da sashe na 2 na dokar EFCC.

Kara karanta wannan

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2

EFCC.
Shugaban EFCC, Olu Olukayode Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: UGC

Me dokar kasa ta ce a kan EFCC

Abin da dokar ta ce shi ne wajibi ga duk wanda zai jagoranci EFCC ya zama jami’in tsaro ko kuma jami’in da ya yi ritaya daga aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani sharadi shi ne ya samu akalla shekaru 15 ya na aikin tabbatar da doka sannan ya kai mataki irin na Kwamishinan ‘yan sanda.

A cewar lauyan, wanda shugaban kasar ya nada bai da alaka da aikin damara, lauya ne wanda bai yi shekaru 15 ya na aiki ba tukun.

Akwai makarkashiya a Hukumar EFCC?

"Bai yi shekaru 15 da su ka wajaba a matsayin jami’ain doka ba. Aikin shari’a da ya yi ba zai zama daya da aikin tabbatar da doka ba.
Halartar taro da kwas a matsayin malamin shari’a ba za su zama daidai da shekaru 15 na aiki da ake nema a sashe na 2 na doka ba.

Kara karanta wannan

Isra'ila Ta Yi Wa Tinubu Alkawarin Ba Da Kariya Kan Rikicin Kasar Da Falasdinu, Ta Fadi Dalilai

Abin da ya ke da shi kurum shi ne wa’adi a matsayin shugaban ma’aikatan ofishin shugaban EFCC, daga baya ya zama sakatare.
Duk aikin da ya yi a hukumar EFCC ba su wuce na tsawon shekaru shida ba. Wannan gwamnati ba ta taba daina ba ni mamaki."

- Daniel Bwala

A kashen maganar da ya yi, mai taimakawa Atiku Abubakar din ya yi addu’a, ya ce watakila an kawo Olukayode ne da wata manufa.

Sabon shugaba a EFCC

Dazu rahoto ya zo cewa Bola Tinubu ya nada sabon shugaban Hukumar EFCC, ya na cewa Ola Olukayede ya yi shekaru 22 ya na aiki.

Sanarwar ta ce tsohon shugaban hukumar watau Abdulrasheed Bawa ya yi murabus. Zuwa yanzu Bawa ya na tsare a hannun hukuma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng