Yan Bindiga Sun Nemi N80m a Matsayin Kudin Fansar Daliban Jami'ar Nasarawa

Yan Bindiga Sun Nemi N80m a Matsayin Kudin Fansar Daliban Jami'ar Nasarawa

  • Yan bindiga sun turo saƙon kuɗin fansar da su ke buƙatar a biya gabanin su sako ɗaiban jami'ar jihar Nasarawa
  • A ranar Litinin da daddare, masu garkuwan suka yi awon gaba da ɗalibai mata huɗu a gidajensu na wajen makaranta a Keffi
  • Wata majiya ta ce a halin yanzu sun kira waya, sun nemi a haɗa musu Naira miliyan 80 jimulla

Nasarawa - Miyagun 'yan bindigan da suka yi garkuwa da ɗalibai mata 4 na jami'ar jihar Nasarawa sun gindaya sharaɗin kuɗin fansar da su ke buƙata kafin su sako su.

Rahoton Leadership ya nuna cewa waɗanda suka yi garkuwa da ɗaiban sun buƙaci a haɗa musu Naira miliyan 80 a matsayin kuɗin fansa.

Yan bindiga sun gaɗi kuɗin fansar ɗaliban jami'ar Nasarawa.
Yan Bindiga Sun Nemi N80m a Matsayin Kudin Fansar Daliban Jami'ar Nasarawa Hoto: Leadership
Asali: UGC

Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton yadda maharan suka yi awon gaba da ɗalibai huɗu a Angwan Ka'are da ke ƙaramar hukumar Keffi, ranar Litinin da ddadare.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Bindiga Suka Salwantar Da Ran Mutumin Da Ya Je Kai Kudin Fansa

Daliban da aka sace sun hada da Rahila Hanya (SLT), Josephine Gershon (Kimiyyar Kwamfuta), Rosemary Samuel (Kasuwanci), da Goodness Samuel (Geography).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindigan sun kai farmaki gidan ɗaliban da ke wajen makaranta da misalin ƙarfe 10:30 na dare, kuma suka yi awon gaba da su.

Yan bindiga sun tutuɓi makusantan ɗaliban

Sai dai a halin da ake ciki, wata majiya ta shaida wa jaridar cewa 'yan bindiga sun kira ɗaya daga cikin masu alaƙa da lamarin, inda suka faɗi buƙatarsu gabanin su saki ɗaliban da suka sace.

A ruwayar Dailypost, majiyar ta ce:

“Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi wadanda suka dace kuma sun bukaci a biya su Naira miliyan 80 domin su sako daliban."
"Jimullar kuɗin fansar ɗaliban guda huɗu shi ne Naira miliyan 80, ma'ana suna neman Naira miliyan 20 kan kowace ɗaliba ɗaya."

Kara karanta wannan

Shiri Ya Yi: Jiragen Yakin Sojin Sama Sun Yi Luguden Wuta Kan Yan Bindiga, Sun Kona Sama da 100 a Jihar Arewa

Ta ce duk da har kawo yanzun ba a cimma matsayar ƙuɗin da za a biya masu garkuwan ba, ana ci gaba da koƙarin ganin an ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.

Ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar ɗaliban jami'ar Nasarawa, Sanata Julius James K, wanda ya tabbatar da haka, ya ce sun maida hankali wajen ceto 'yan uwansu.

Yan Bindiga Sun Halaka Basarake, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Yawa a Niger

A wani rahoton na daban kuma Yan bindiga sun yi ajalin Basarake, sun kwashi jama'a sun yi awon gaba da su a ƙauyukan jihar Neja ranar Talata.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Neja ya tabbatar da kai sabon harin amma ya ce har yanzun bai samu cikakken rahoto ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262