Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 a Wani Sabon Hari a Taraba

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 a Wani Sabon Hari a Taraba

  • Ƴan bindiga da ake kyautata zaton mayaƙan wata ƙabila ne sun kai wani hari a wata kasuwa cikin jihar Taraba
  • Ƴan bindigan sun halaka mutum biyu a yayin harin tare da kwashe kayayyakin miliyoyin nairori a ya yin harin da suka kai
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar harin inda ta ce ta cafke wasu da ake zargin suna da hannu a kai harin

Jihar Taraba - Wasu ƴan bindiga da ake zargin mayaƙan wata ƙabila ne sun kai hari kasuwar Didango da ke ƙaramar hukumar Karim-Lamido a jihar Taraba.

Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a kasuwar sun salwantar da rayukan mutum biyu.

Yan bindiga sun halaka mutum biyu a Taraba
Yan bindiga sun kai hari cikin wata kasuwa a Taraba Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Hakazalika an jikkata mutane da dama tare da kwashe kayayyakin miliyoyin naira yayin harin.

Wani mazaunin garin, Yakubu Adamu, ya shaida wa Daily Trust a wata hira ta wayar tarho cewa ƴan bindigan dauke da muggan makamai sun kai hari garin ne a ranar Laraba, wacce ta kasance ranar kasuwa da misalin ƙarfe 9:00 na dare.

Kara karanta wannan

Shiri Ya Yi: Jiragen Yakin Sojin Sama Sun Yi Luguden Wuta Kan Yan Bindiga, Sun Kona Sama da 100 a Jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Maharan sun fito ne daga wani kauye da ke kusa da mu. Babu wanda ya tunzura su saboda al'ummar Digango waɗanda galibinsu ƴan kabilar Wurkum, Jarawa da Hausa-Fulani ne ba su da wata takaddama da kauyen da maharan suka fito da har za su kawo mana wannan harin."

Sai dai Adamu ya ce matasan garin sun dakile harin inda aka tilastawa ƴan bindigan tserewa zuwa kauyensu wanda ke da nisan kilomita huɗu daga Didango.

Wani mazaunin garin Bello Dauda ya bayyana cewa harin da ƴan bindigan suka kai wani yunkuri ne na sake haifar da sabon rikicin ƙabilanci a yankin.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ya ce mutum ɗaya ne ya mutu sannan wasu biyar suka samu raunika.

Ya ce an kama mutane biyu da ake zargi da kai harin, inda ya ce suna taimakawa ƴan sanda wajen gano wadanda suka kitsa kai harin.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wasu Garuruwa, Sun Halaka Babban Basarake a Jihar Arewa

An Yi Awon Gaba Da Masu Rakiyar Gawa

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu mutane da ke kan hanyarsu ta kai gawa a maƙabarta a jihar Kogi.

Malamin addinin musulunci, Alfa Fasasi Ola da ɗan uwansa na ɗaga cikin waɗanda ƴan bindigan suka yi awon gaba da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel