Idan Kazo Borno Baka Kashe Dan Boko Haram Ba Baka Cika Soja Ba, CDS Ga Sojojin Najeriya
- Christopher Musa, Babban Hafsan Tsaro na Najeriya, ya zaburar da dakarun sojojin Najeriya da ke yaki da yan ta'adda a jihar Borno
- Musa ya fada wa sojojin cewa su dena zama suna jira sai yan ta'adda sun kawo hari kafin su dakile, amma su tashi su rika farautarsu kafin su kawo hari
- Shugaban sojojin ya kuma ce duk wani soja da ya tafi Borno bai kashe a kalla dan Boko Haram daya ba bai cika soja ba
Maiduguri, Borno - Babban Hafsan Tsaro, CDS, Christopher Musa, ya umurci dakarun sojojin Najeriya su nemi yan ta'addan Boko Haram su kashe su kafin su kai wa yan Najeriya hari.
Musa ya bada wannan umurnin ne ga dakarun Operation Hadin Kai a sansanin Maimalari, Maiduguri, babban birnin jihar Borno, rahoton Tribune.
Isra'ila v Falasdinu: Shahararren Malamin Addini Ya Bayyana Matsayarsu Akan Wannan Rikici, Ya Tura Sako
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CDS din ya ce duk wani soja da ya zo sansanin kuma bai kashe a kalla dan Boko Haram daya ba bai cika soja ba.
Sai Ka Kashe Dan Boko Haram Za Ka Cika Soja, CDS Ga Sojojin Najeriya
Ya zaburar da sojojin su dena jiran yan ta'addan, yana mai cewa:
"Kada kawai ku taho ku yi barci a sansani, ku tabbatar kun nemi yan Boko Haram kun kashe su. Duk wanda ya taho sansani ya gama aikinsa ba tare da kashe a kalla dan Boko Haram daya ba bai cika ba.
"Don haka ku tabbatar kafin su tafi, ku neme su, wannan ne kadai hanyar da za mu iya karar da su baki daya.
"Bai kamata su rika neman mu ba, mu ya dace muna nemansu. Ka da ku tafi su zauna har sai sun kawo hari kafin ku dakile, babu batun dakile hari, ku tafi ku neme su ku kashe su."
Shugaba Tinubu na muku fatan alheri, Musa ya fada wa sojoji da ke yaki da Boko Haram
Ya kuma sanar da sojojin cewa Shugaba Bola Tinubu yana gode musu bisa kokari da sadaukarwa a yakin da suke yi da yan ta'adda a kasar.
Ya kara da cewa:
"Shugaban kasa yana murna da mu kuma yana mana fatan alheri,
"Ya kuma tunatar da mu cewa da saura amma muna kan hanyar dai-dai. Idan muka cigaba kan hanyar da muke, nan bada dadewa ba za mu kawo karshen Boko Haram."
Sojoji Sun Sheke Kasurgumin Dan Ta'adda a Jihar Zamfara
Dakarun sojojin Najeriya sun kashe wani kasurgumin dan ta'adda da ya addabi mutanen yankin Arewa maso Yamma tsawon lokaci.
Dakarun sojojin sun samu nasarar halaka Ummaru Nagona, wanda yayi ƙaurin suna wajen ta'addanci a yankunan jihohin Sokoto da Zamfara, Daily Trust ta rahoto.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2
Asali: Legit.ng