Yan Sanda Sun Kama Matashi Dan Shekaru 19 Da Ya Binne Kaninsa Da Rai
- Yan sanda sun cika hannu da wani matashi dan shekaru 19 wanda ake zargin ya binne dan ubansa, Friday Oshhodi, da ransa
- Rundunar yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da kama Goodness Oshodi, wanda ya binne kaninsa bisa umurnin mahaifiyarsa a ranar Laraba
- Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, a garin Apamisede da ke karamar hukumar Adabi ta jihar Kogi
Jihar Kogi - A ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba, rundunar yan sandan jihar Kogi, ta sanar da kama Goodness Oshodi, matashi dan shekaru 19 wanda ake zargin ya binne dan ubansa, Friday Oshhodi, da ransa bisa umurnin mahaifiyarsa kan sace N10,000.
Yadda Friday Oshhodi ya binne kaninsa a jihar Kogi
Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, lamarin ya afku ne a yammacin ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, a garin Apamisede da ke karamar hukumar Adabi ta jihar. Sai dai makwabta sun yi nasarar ceto shi.
A cewar wasu ganau, kishiyar uwar yaron ce ta umurci babban danta da ya hukunta Friday kan sace mata N10,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake aiwatar da umurnin mahaifiyarsa, yayan yaron ya fara yi masa jina-jina kafin ya yanke shawarar binne shi da ransa.
Goodness ya fadi dalilin da yasa ya binne kaninsa da ransa
Da yake magana kan dalilin da yasa ya binne kaninsa da ransa, Goodness ya ce ya aiwatar da umurnin da mahaifiyarsu ta bayar ne.
Goodness ya kara da cewar koda dai mahaifiyarsa ta tafi coci amma ta bar masa umurnin cewa ya hukunta kanin nasa.
Rundunar yan sandan Kogi ta yi martani yayin da aka binne yaro da ransa
Da yake martani, kakakin rundunar yan sandan jihar, SP William Aya, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce an kama yaron kuma yana amsa tambayoyi, rahoton Vanguard.
"Eh muna sane. An kama yaron, ana gudanar da bincike kan dalili da yadda irin wannan abu ya iya faruwa," cewarsa.
Kotu ta yankewa yar TikTok shekaru 2 a yari kan zagin shugaban kasa
A wani labarin kuma, mun ji cewa kotun kasar Angola ta tura wata yar TikTok mai suna Ana da Silva Miguel, gidan yari na tsawon shekaru biyu kan zagin shugaban kasarsu, João Lourenço.
Da farko kotun ta yankewa shahararriyar yar TikTok din da aka fi sani da Neth Nahara, hukuncin watanni shida a gidan yari a watan Agusta.
Asali: Legit.ng