Idris Alubankudi Saliu: Bayanai 10 Game da Sabon Hadimin Bola Tinubu
- An tabbatar da Idris Alubankudi Saliu a matsayin wanda zai rika ba Mai girma Bola Ahmad Tinubu shawara
- Kafin nadin, mutane da yawa sun san ‘dan kasuwan a bangaren tattalin arziki da fasahar zamani a kasashen duniya
- Kwanaki Idris Alubankudi Saliu ya samu makusan miliyoyin daloli da Interswitch su ka saye wani kamfaninsa
Abuja - Zuwa yanzu labari ya ratsa ko ina cewa Idris Alubankudi Saliu ya samu mukamin mai bada shawara a fadar shugaban Najeriya.
Sanarwa ta fito cewa Alubankudi Saliu ya zama mai ba shugaba Bola Tinubu shawara.
A rahoton nan, mun tattaro gajeren bayani ne a game da Malam Idris Alubankudi Saliu kamar yadda ya zo a shafin TechCabal kwanaki.
Wanene Idris Alubankudi Saliu?
1. Idris Alubankudi Saliu ya yi suna wajen kasuwanci da wayar da kan al’umma a game da fasahohin zamani a Najeriya da sauran kasashe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Alubankudi shi ne shugaban sashen fasaha (CTO) na kamfanin Interswitch Group wanda ya ke da dadadden tarihi fadin nahiyar Afrika.
3. Kwararren masanin ya samu aiki da Interswitch Group ne ta hanyar mallakar kamfaninsa na Vanso da aka yi a wata yarjejeniya mai tsoka.
4. Kafin a saida kamfanin Vanso, rahoton ya nuna ya na da rassa a Legas (Najeriya), Capetown (Afrika ta Kudu) da birnin Wurzburg (Jamus)
5. A jami’ar Columbia da ke New York a kasar Amurka, Saliu Alubankudi ya samu digirin farko a ilmin kimiyyar komfuta a shekarun baya.
6. Crunch base ta ce daga baya ya koma jami’ar domin yin digirgir a ilmin na komfuta.
7. Yanzu haka shi ne shugaban kamfanonin Arca da Ceviant wanda su ke aiki har a kasashen ketare, sun yi aiki da irinsu Dantata da Wakanow.
8. A tsawon shekaru kusan 20 ya nuna kwarewarsa a bangarorin sadarwa, fasahar zamani, hanyoyin kudi da kuma tattalin arzikin zamani.
9. Baya ga Ceviant Finance, Idris Alubankudi Saliu ya yi aiki a kamfanoni da-dama, ana sa ran zai bada gudumuwa ga gwamnatin Najeriya.
10. A ranar 11 ga Oktoban 2023, Bola Tinubu ya nada shi cikin jerin hadiminsa.
Layin fetur ya dawo Najeriya
A farkon makon nan aka ji shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kolo Kyari ya yi bayanin abubuwan da su ka jawo danyen layin man fetur.
Malam Mele Kolo Kyari yake cewa sun magance matsalolin da su ka jawo hakan.
Asali: Legit.ng